Fitowar Al’ummar Jihar Kano Yin Katin Zaɓe Na Da Matuƙar Muhimmanci -Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

An bayyana cigaban da ake samu a zuwan gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf a bayyane suke ba a ɓoye ba mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin siyasa, Hon. Sunusi Kwankwaso ne ya bayyana hakan.

Ya ce cikin shekara biyu ‘yan fansho na amfana, masu albashi ma’aikata 22 zuwa 23 ga wata ake soma biyan albashi su sami kuɗinsu ba tare da sassaƙa ko zaftara ba.

Ya ƙara da cewa ga ɗaukar ma’aikata da aka yi da tura ɗalibai makarantu a ciki da wajen ƙasar nan aka buɗe manyan makarantu da aka rufe shekara 8 a gwamnatin Ganduje. Daga irin cigaban da aka samu akwai gyara makarantu da auren gata da sauran aikace-aikace da ake ta gudanarwa wanda Gwamna shi kansa ba zai iya lissafa su ba a lokaci guda.

Ya ce game da masu cewa gwamnatin ta gaza Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso ya ce shi maƙiyi ko ruwa ka shiga zai ce ka tayar da ƙura ne, saboda haka ƙashin kaji ko’ina yake sai a ɗebo a yaɓa maka, amma wanda ake faɗawa shi mai hankali ya san abin da aka yi kuma duniya ta sani duk abin da ake yi na alheri a wannan gwamnati idan wasu masharranta sun shiga ɗaki sun ƙulla sharri komai daɗewa gaskiya za ta bayyana.

Ya yi nuni da cewa ba su san da wasu ‘yan adawa da suke cikin gwamnati suke leƙen asiri ba, kuma su tafiyarsu tsarkakkiyace a Kano, hanya ɗaya ce, kuma duk wanda yake Kwankwaso da Kwankwasiyya da Injiniya Abba Kabir Yusuf baya tunanin yin abin da bai kamata ba, tafiya ake cif da cif tsaf.

Jam’iyyasu ta NNPP me littafi da hular digiri mai ja da fari a haka ake jajircewa ake aiki tuƙuru da ɗaukaka ilimi da koyar da tarbiyya.

Ya ce masu adawa da Kwankwaso tun ba a shiga NNPP ba wane irin surutu ne PDP ba ta yi ba cewa Kwankwaso zai bar PDP ya koma APC haka APC ta yi ta cewa zai dawo APC amma ya kafa DNM daga nan ya shiga NNPP.

Saboda idan mutum ya riƙa, kowa idan ya ci abinci ya miƙe ƙafa sai ya faɗi abin da yake so. Amma koma mene ne lokaci ne zai nuna amma yanzu Kwankwaso yana nan a NNPP da ita suka shiga zaɓe suka ci.

Hon. Sunusi Surajo ya ce masu yin ƙorafi da za a ce wai mutumin da yake jihar Ribas yake Kwankwasiyya ya ce an manta da shi bai yarda da wannan ba, domin shi ya yi wakilci zuwa jihar Ribas, kuma mutane daga Ribas daban-daban sun zo da kokensu an share musu hawaye.

Ya ce domin idan mutum ya san siyasa yana yin ta, zancen ma ba ka da gwamnati a Ribas ka ce Kwankwasiyya ta manta da kai kamar ka yaudari kai ne in a Ribas kake Kwankwasiyya, ba ma can ba duk ƙasar nan duk abin da ya sami ɗan Kwankwasiyya, Kwankwaso na takawa da kansa ya je nema musu haƙƙi har Ribas Kwankwaso ya je nema musu haƙƙi, wannan ta ba su darajar zama su miƙe ƙafarsu.

Mai bai wa Gwamnan jihar Kano shawara a kan harkokin siyasa ya ce abin da ya sa ake zaɓar gwamnati shi ne ta yi aiki da mutane za su amfana, ba lallai sai kai kaɗai an amfanar da kai ba, wanda ya san siyasa ba ya ƙorafi na cewar ya wahalta ba a kula shi ba, ya tabbatar ‘yan Kwankwasiyya na jihar Ribas da sun zo ya taimaka musu, kuma suna zuwa wajen waɗaansu irin sa, in ka gamu da mutum ka ji ya ce da kai yana Ribas ba a taimake shi ba, ko shi ne shugaban matasa su ba su ji daga bakinsu ba, kuma sun san ɗan Kwankwasiyya ba zai yi wannan kalmar ba, duk inda yake in dai Kwankwasiyya yake da gaske.

Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso ya yi kira ga al’ummar jihar Kano gaba ɗaya ba tare da bambanci ba, su fita su yanki katin rijista na zaɓe, wanda ba shi da ita da wanda nasa ya ɓata ya gyara.

Jihar Kano da ake da yawan al’umma fiye da kowa a ƙasar nan bai kamata a mayar damu baya ba.

Ya kamata mu fita mu a jawo hankalin mutane su yi ƙoƙarin karɓa don za ta kai wata rana ko tafiya za ka yi zuwa wani waje, ko wani abu ya zo na ƙaruwa a ce sai an ga katin zaɓenka domin da katin zaɓe da na ‘yan ƙasa suna da muhimmaci mutane su dage su yi.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum