Daga Ibrahim Muhammad.’
Shugaban shiyya na Hukumar kare haƙƙin mallaka na ƙasa (Copy Right Commission) mai kula da jihohin Kano, Katsina da Jigawa, Malam Sani Ahmad ya bayyana cewa hukumarsu ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Farfesa John Essen akwai aikace-aikace da Hukumar take na ilmantar da masu ruwa da tsaki a harkar haƙƙin malaka.
Ya bayyana haka ne a yayin taron ƙarawa juna sani da Hukumar ta gudanar da haɗin gwiwa da ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen Ungogo a ranar Litinin a ɗakin taro na Babbar Kotun jihar Kano.
Ya ce sashen ilmantarwa na Hukumar ne suka shirya wannan taron bita domin ilmantar lauyoyin reshen ungogo jihar Kano a kan abin da ya shafi kare haƙƙin mallaka, dokoki da kuma dukkan abubuwa da ya kamata su sani a kan abin da ya shafi kare haƙƙin mallaka.
Ya ce a yanzu akwai sashe a cikin kundin dokokin Hukumar da aka sabunta shi a 2022 da ya zo da sabon sashi na abin da ya shafi ayyukan fasaha da ke kan yanar gizo da a baya babu doka a kai, dokar sabuwa ce da yawanci lauyoyin nan sune idan mai haƙƙi ya sami matsala yana sa lauyoyi domin zuwa kotu neman haƙƙinsa.
Don haka Hukumar ta shirya wannan taro domin a faɗakar da lauyoyi kan sabon sashe na dokoki don kare haƙƙin mallaka wanda ya shafi yanar gizo, kuma an yi musu bayani yadda duk wani aiki da yake kan internet ga yadda ake kare shi da yadda ake tsare shi daga sata kuma in an yi maka satar ga matakai da za ka ɗauka na neman haƙƙi an yi musu bayani filla- filla sun gamsu sun yi farin ciki a kai.
Ya ce Hukumar ta kare haƙƙin mallaka ta ƙasa reshen jihar Kano ta gamsu da ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen Ungogo ta jihar Kano bisa amincewa da goyon baya da suka ba su aka gudanar da taron da su ma suka yaba a kai.
Malm Sani Ahmad ya ce fatansu a Hukumar shi ne duk wani mai haƙƙi na mallaka ɗan ƙasar nan duk inda yake a duniya ya zama cewa Hukumar ta kare masa haƙƙi daga yin amfani da aikinsa ba bisa ƙa’ida ba, wanda hakan kan iya jawo masa asara ta kuɗi da kuma wani abu makamancin haka, burinsu ‘yan Nijeriya su sami mafita da kuma tsira daga satar fasahar da ake musu a kan ayyukansu, kuma suna samun nasara a kan hakan.
Shi ma da yake bayani game da taron bitar shugaban ƙungiyar lauyoyi na ƙasa reshen Ungogo jihar Kano, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce taron an yi shi ne domin ya zama lauyoyi sun san abin da yake tattare da dokokin ayyuka na rubuce-rubuce ko na littattafai ko na wani rubutu da mutum zai yi ya san ta yaya zai kare shi daga masu kutse ko kuma masu yin jabun kwafin rubutunsa ko wani aikinsa, mene ne doka ta shimfiɗa ina zai je ina ne matsayar sa? Mene ne kuma zai jawo karya ƙa’idar rubutun da kuma yadda doka ta tanada matakai da mutum zai ɗauka.
Da yake tsokaci a kan masu amfani da fasahar zamani wajen yin hukunci da fasahar zamani a yanzu abu ne da ya zo wa ɗan’adam, kuma duk lokacin da cigaba ya zo masa ya karɓe shi hannu bibbiyu, sai dai ya ja hankalin lauyoyi kan duk lokacin da suka yi amfani da wata fasahar zamani su tabbatar sun tace sun tabbatar da tsaftarsa da gaskiyarsa ta hanyar bincike da duba waɗansu takardu da za su tabbatar da abin da suka samo na bayani da binciken fasahar zamani daidai yake ba ba abu ne mara sahihanci ba.
Ya ƙara da cewa suna so mambobinsu su zama suna da masaniya a kan duk abubuwan da ya shafi haƙƙin mallaka walau na rubutu ne ko na wani abu na kasuwancinka da ka yi kayanka yaya za ka kare shi, kuma shi Lauya ya ya zai wakilci wanda yake tsayawa idan an sami shisshigi ko wani ya yi jabun aikinsa ko kuma an masa kutse ba tare da izini ba yaya Lauya zai ƙare shi ya ba shi shawara yadda zai tafiyar da haƙƙin nasa ko zai neme shi ko zai wani abu da ya shafi wannan harkar.
Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce a matsayinsu na ƙungiyar lauyoyi wanda sukan so su shiga kowane ɓangare da ya shafi rayuwar ɗan’adam suka ga ya dace su yi haɗin gwiwa da Hukumar da take kare haƙƙoƙin mallaka suka shirya wannan taron bitar ga mambobinsu
Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce shi hukunci a hannun kotu yake, to amma idan wata Hukumar doka ta kafa ta ta ce ita za ta kula da wani ɓangare na rayuwar ɗan’adam shi ne matakin farko da ya kamata a fara bi kafin ka garzaya ka tafi kotu in kuma an sami abin da ya fi ƙarfin wannan Hukumar to shi ne daga baya za a tafi gaban kotu.
Taron ya sami halartar mambobin ƙungiyar da dama da suka saurari muhimman bayanai kan sani dokokin haƙƙin mallaka.







