Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hon. Kabiru mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulƙadir a kan al’amuran da suka shafi cikin Gida (P.A Domestic), ya bayyana jin daɗinsa da gode wa Allah bisa karramawa da ƙungiyar cigaban Ɗambatta da Makoɗa suka yi masa kan irin tallafi da suka ga yana yi ga cigaban ƙananan hukumominsu.
Ya ce karramawar ta ƙara masa karsashi da sake yin hoɓɓasa wajen cigaba da ayyuka na alheri da yake aiwatarwa. Ya ce a yanzu zai nunka fiye da abubuwan da yake yi a baya, “Domin in har al’umma sun ga ka yi abin alheri suka karrama ka a kai, to ka ƙara ƙoƙari don shaidar duniya ita ce ta kiyama,” ya bayyana.
Hon. Kabiru P.A ya ce, duk da cewa shi ɗan asalin Ɗambatta ne da yake zaune a jihar Bauchi suna zaman lafiya da har yake bayar da gudunmawa ta alkhari a siyasar jihar, kasancewar Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Abdulƙadir sananne ne a Nijeriya baki ɗaya wajen ayyukan alheri.
Ya ƙara da cewa suna tafiya tare da Gwamnan Bauchi Sanata Bala duba da irin alhairansa, domin shi mutum ne da yake yin ɗimbin ayyuka na cigaban al’umma da yardarsa suke bayar da gudunmawa ga jihar Bauchi har suke ba da gudunmawa ta alkhari da ya shafi Ɗambatta da Makoɗa.
Binciken da AMANA ta gudanar ta gano cewa, irin ayyukan alkhairin da ƙungiyar cigaban Ɗambatta da Makoɗa suka ga Hon. Kabiru Muhammad yana yi har suka karrama shi sun haɗa da aikin gina masallatai, taimakawa marayu da sauran mutane masu ƙaramin ƙarfi, ta hanyar gyara musu muhallinsu da ya rushe da taimaka wa makarantun Islamiyya da na boko da biyan buƙatun matasa a fannonin gina cigaban rayuwarsu.






