Iyalan Tsohon Gwamnan Jihar Kano Ganduje Ba Su Da Hannun Jari A Tashar Tsandauri Ta Dala -Adamu Sanda

Tashar tsandauri ta Dala (Dala Inland Dry Port) ta musanta wani iƙirarin gwamnatin jihar Kano na cewa wasu daga iyalan tsohon Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin masu hannun jari a kamfanin.

Wannan na cikin wata sanarwa da Sakataren kamfanin Tashar Tsandauri na Dala, Alhaji Adamu Sanda ya fitar a ranar Laraba a Abuja ya ce batun ba shi da tushe bare makama.

Ya ce iyalan na Ganduje ko gwamnatin jihar Kano ba su mallaki wani kason hannun jari a kamfanin ba.

Bayanai daga Hukumar yi wa kamfanoni rijista na ƙasa CAC da Hukumar Gudanarwar kamfanin ya tabbatar babu wani a iyalan Ganduje da ya mallaki hannun jarin.

Sannan sanarwar ta musanta cewa gwamnatin jihar Kano na da hannun jarin kaso 20 na kamfanin, kuma ba ta da wani wakili a gudanarwar kamfanin Tashar Tsandauri ta Dala.

Wannan sanarwar ta biyo bayan iƙirarin da Hukumar Ƙorafe-Ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta yi kan zargin karkatar da kuɗin jihar Naira biliyan huɗu zuwa Tashar Tsandauri a zamanin mulkin Ganduje.

Hukumar karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta yi zargin cewa an fitar da kuɗin ne a 2020 da sunan za a samar da ababen more rayuwa ga tashar duk da cewa an yi zargin jihar Kano na da kaso 20 cikin 100 na kuɗaɗen da aka tura su ga iyalan Ganduje da aka tura kuɗin ga daraktoci da masu hannayen jari tare da cire jihar Kano.

Shugaban Hukumar Ƙarɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Rashawa na jihar Kano, Sa’idu Yahaya ya ce suna aiki da ƙorafe-ƙorafen al”umma da ke zargin an yi almubazzaraci da kuɗaɗe masu yawa da suka shafi aikin na Tashar Tsandauri ta Dala.

Hukumar ta ce tuni bincike ya yi nisa inda aka gayyaci mutane da dama domin yi musu tambayoyi a kai.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo