Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na Goma Na Aikin Jinya Kyauta, An Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kammala zagaye na goma na shirinta na musamman na aikin jinya kyauta, inda aka kula da marasa lafiya 3,447 daga sassa daban-daban na jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce shirin wanda aka fara shi tun watan Yuli na bara, yana bayar da jinyar kyauta ga marasa lafiya da ke fama da cuta irin su ciwon ido (cataract), kumburin mafitsara ko gambon ciki (hernia da hydrocele), da kula da masu yoyon fitsari na ‘vesico-vaginal fistula’ (VVF) tare da faxakar da jama’a kan kiwon lafiya.

An gudanar da zagayen jinya na goma a asibitoci kamar Asibutin Ƙwararru na Yariman Bakura, Babban Aaibitin Gusau, Aisbitin Ido na Gusau da Aaibitin Farida.

Sanarwar ta ce, “Domin rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta wajen samun kula da lafiya, gwamnatin Dauda Lawal ta ƙaddamar da wannan shiri na musamman domin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da ke buƙatar jinya.”

Shirin, wanda aka fara a watan Agusta 2023, ya riga ya isa ga marasa lafiya sama da 3,400 zuwa asibitoci daban-daban ta hanyar tsarin tele-screening, wanda ke bai wa ƙwararrun likitoci damar lura da marasa lafiya daga ƙauyuka da yankunan karkara cikin gundumomi 14 na jihar.

Bangarorin da aka kula da lafiya a zagaye na goman da suka haɗa da; mutum 1,659 marasa lafiya masu kumburin ciki da irin sa. Mutum 1,081 masu ciwon ido da aka yi wa tiyata. Mutum 118 marasa lafiya masu cutar VVF da aka yi wa tiyata.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan shiri ya zama wata nasara ga gwamnatin jihar wajen kai ingantacciyar kulawar lafiya ga jama’a, musamman a yankunan da ke da ƙarancin cibiyoyin jinya.

Sulaiman Bala Idris
Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara
Oktoba 21, 2025

Related Posts

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum