
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da Christopher Nduka a gaban mai shari’a Farook Lawal Adamu na babbar kotun tarayya da ke Kano a kan tuhume-tuhume guda uku da suka hada da zamba cikin amincin.
Da ake karanta masa tuhume-tuhumen da ake masa, an ce: “Kai, Christopher Nduka, a wani lokaci a cikin watan Satumba, 2022 a Kano, jihar Kano, ka samu Naira miliyan biyu da dubu dari takwas da hamsin (N2,850,000) mallakin wani Tochukwu Obinna Chioke na biyan kudin siyan kayayyakin harhada magunguna da ka san karya ne, kuma ya aikata laifin da ya sabawa sashe na 1(1)(b) da kuma sashe na 1(3) na kudin hukunta laifin zamba ta 2006.”
Kotun ta zargi Nduka da cewa ya bayar da cakin kudi miliyan daya, Naira dubu dari takwas (N 1,800,000,00) a madadin wani Chioke Tochukwu Obinna, daga baya ta bayyana zamba ce saboda isassun kuɗi a cikin asusun ajiyar.
Kotun ta ce kuma ta tabbatar da cewa laifin ya saba wa sashe na 1 (1) (b) na Dokar Hukunta Laifi ta Jihar Kano.
Lokacin da aka karanta masa tuhumar da ake masa ya musanta tuhume-tuhumen da ake masa.
Lauyan masu gabatar da kara, Idris I. Haruna ya roki kotun da ta dage zaman shari’a bisa rokon wanda ake kara.
Lauyan da ake kara, P.A Edamaku ya roki kotun da ta ba da belin wanda yake karewa har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar.
A sakamakon haka mai shari’a Lawal ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira Miliyan daya da kuma mutum daya da zai tsaya masa wanda dole ne ya mallaki kadarorin da ke karkashin ikon kotun.
Ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 27 ga Maris, 2024 domin fara shari’ar.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Nduka, wani dan damfara ne da aka yanke wa hukunci har sau biyu a baya bisa laifuka makamantan haka.
An sake kama shi a lokacin da mai shigar da kara ya yi zargin cewa ya karbi kudi har Naira miliyan 2,850 da sunan a kawo masa kayayyakin harhada magunguna, amma ya karkatar da kudin don amfanin kansa.







