Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Shugaban shiyya na hukumar kula da ingancin kaya na kasa “SON” na shiyyar Kano da Jigawa Mista Albart Wilberforce ya bayyana cewa karkashin jagorancin shugaban hukumar na kasa.Hon.Yahuza Ado Yankaba zasu cigaba da aiki da hadin kan kamfanoni da sauran jama’a masu samar da kayyaki don tabbatar da yin masu inganci.
Ya bayyana haka ne a taron ranar Ingancin kaya ta Duniya bayan Wani gangami na jerin gwano da suka shirya da ya sami halartar dinbin kamfanoni na jihar Kano da Jigawa.
Ya ce za a samu cigaba a harkar kasuwanci da masana’antu bisa kokarin Shugabanin Hukumar kuma zasu cigaba da yin irin wannan taruka don samun cimma nasarar samarda kaya masu inganci.
Ya ce taron na Duniya ne kuma kasancewar Kano cibiya ce ta kasuwanci an gudanar ta taron fiye da na sauran jihohi a kasar nan kuma suna samun hadin kai da goyon bayan masu masana’antu da yan kasuwa wajen samar da kaya masu inganci.
Ya ce yanzu haka akwai kayyaki da suka kai 50 da keda sahalewar hatinin ingancin kaya na hukumar ta “SON”A jihar Kano kuma sun halarci taron tare da bada gudunmawa ta fannoni da dama wajen samun nasarar gudanar da taron.
Mista Albart Wilberforce daraktan na shiryyar Kano da Jigawa na hukumar “SON “ya ce sun godewa Gwamnatin jihar Kano da masu kamfanoni da goyon bayan da suke baiwa hukumar hakan ne tasa suke samun nasara kuma abinda suke alfahari dashi daga mutanen Kano shine duk lokacin da suka je ga masu masana’antu sukan nuna musu abinda yakamata suyi kuma suna yi suna tsare ka’ida.
Da yake bayani game da taron daraktan Kamfanin AUG Legacy Malam Musa Sadik a madadin shugaban kamfanin Alhaji Ali Kalaba yace suna tabbatar da inganci da adadin yawan abinda suke ba tare da gibi ba don tsare gaskiya da inganta lafiyar al’umma daga mai da muke samarwa.
Ya ce yanzu haka kuma kamfanin na da ma’aikata na dindindin da ke aiki kai tsaye wajen guda 15 da kuma na wucin gadi da sun fi guda 100 suna kuma tsare dukkan ka’idodi na hukumar ingancin kaya ta kasa.
Shima manajan kula da sarrafa kaya na kamfanin yin katifu na Alwala dake garin Zainawa a Kano.Aliyu Muhammad Shehu ya ce sun godewa Allah ganin cikin kamfanin masu yin abubuwa an sami gayyatar kamfanin taron na ingancin kaya kuma sun gamsu da aikin hukumar “SON”
Aliyu Muhammad Shehu
ya yi nuni da cewa Kamfanin Katifa na Alwala a jihar Kano yake amma amma katifar ta kai inda su ma basu je ba duk wanda ya ga katifar Alwala a inda yake ita takai kanta saboda nagarta da take da ita.Sannan suna da kyakkyawan fahimta da al’ummar wurinda kamfanin yake suna samun addu’a saboda gamsuwa da aminci da abinda suke.







