An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 100 Da Soma Saukar Jirgin Sama A Kano -Sa’ad Sa’id Sa’ad

Daga Ibrahim Muhammad

An gudanar da da taron cikar shekara 100 da fara saukar jirgin sama na farko a Kano tare da karrama wasu muhimman mutane da suka bayar da gagarumar gudummawa ga bunƙasa harkar sufurin jirgin sama a Kano da ma ƙasar nan baki ɗaya a yayin bikin.

Taron ya kasance na haɗin gwiwa ne da makarantar horar da harkokin ayyukan jiragen sama na Caliphate Aviation da ke Kano da hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa FAAN ya samu halartar ɗimbin mutane, masana da kuma ɗalibai da waɗanda suka ba da gudunmawa a harkar jirgin sama.

Alhaji Sa’ad Sa’id Sa’ad (SSS) shugaban kwamitin shiryawa da gudanar da taron, kuma shi ne shugaban makarantar Caliphate Aviation da ke Kano a zantawar da ya yi da ‘yan jarida bayan ƙarƙare taron inda ya bayyana cewa soma saukar jirgin sama na farko a Kano shekara 100 shi ya buɗe duk wata harka da aka gina da ta shafi cigaban harkar jirgin sama, ba kawai a Kano ba amma faɗin ƙasar nan da yammacin Afirka gaba ɗaya.

Ya yi nuni da cewa duba da wannan, ta sa a ƙoƙarin makarantar Caliphate Aviation da suke zartarwa ta koyon karatun da ya shafi tashi da saukar jirgin sama da ke Kano suka ga akwai buƙatar jawo hankalin mutane a yi murna a wannan rana, domin itace hanya da za a yi wa Allah godiya da jawo hankalin mutane kan wannan baiwa da Allah ya yi wa Kano.

Ya ce akwai dalili da Allah ya zaɓi jirgin saman ya soma sauka a Kano shekaru 100 da suka gabata, wanda alhali kuma zai iya sauka a ko’ina, don haka ya kamata mu yi duba a kan hikimar hakan da irin baiwa da Allah ya yi mana, mu duba mu ga wani alheri da ƙalubale aka samu.

Abokanmu da aka soma tare a wane mataki suke, mun kai inda suke? Idan ba mu kai ba mene ne dalilin hakan ya za a yi mu kai, za mu iya ko ba za mu iya ba? Za mu iya taimakon kanmu ko muna can muna jira ta neman taimako a waje na abin da kuma za mu iya yi wa kanmu.

Alhaji Sa’ad Sa’id Sa’ad ya ce, “Mun fahimci wannan filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Malam Aminu Kano da Allah ya ba mu a Kano tamkar wata ƙofa ce ta Azurfa da za mu iya buɗewa. Ita ce kaɗai filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa a Arewacin ƙasar nan wadda jihohin Arewa fasinjojinsu ke zuwa su tashi ya kamata a duba ta yaya za a yi amfani da ita domin ta mahaifar da samar da ayyuka ga matasa. Yanzu filin jirgin saman babu abin da babu, ba harkar da ba za ka iya yi ba.”

Ya ce shi ya sa ma daga mutanen da suka karrama a wajen taron an yi ƙoƙarin jawo hankalin mutane su gane duk ƙanƙantar aiki babu ƙarami tunda wani da shi yake neman abinci, don haka aka girmama masu ƙananan sana’o’i a filin jirgin saman, saboda a nunawa mutane wani abu ne da a duk abin da kake, wasu nasa ido kuma suna yi wa Allah godiya, kuma suna ganin girmanka a kai.

Alhaji Sa’ad Sa’id Sa’ad ya bayyana mutuƙar gamsuwa da samun nasarar gudanar da taron da ya haɗa masu ruwa da tsaki, kama daga malamai masu nazari na ilimi daga jami’o’i daban-daban da suka halarta daga Jami’ar Bayero da ta ABU Zariya da Jami’ar Sufuri ta Ƙasa da ke Daura da Jami’ar Abuja, sun zo sun kuma gane cewa akwai buƙatar a karkato hankali kan masana’antar tashi da saukar jirgin sama a yi bincike na ƙwararru a sami tabbatattun alƙaluma don a zuba jari mai yawa a wannan harkar ta jirgin sama.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum