Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hadimi na musamman ga mataimakin shugaban Majalisar Dattawa na ƙasa Sanata Barau I. Jibrin a kan harkar kasuwannin waya, Ambasada Ibrahim Rabi’u Tahir ya yi kira ga jam’iyyarsu ta APC ta bai wa Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin tikitin takarar Gwamnan jihar Kano in Allah ya kai mu 2027.
Ya bayyana haka ne bayan wani gangami da ‘yan jam’iyyar APC da suka ƙunshi Dattawan jam’iyyar da tsofaffin ‘yan majalisu na jiha da na tarayya da tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi suka yi don tabbatar goyon bayansu da yarda da cancantar Sanata Barau I Jibrin ya yi takarar Gwamna a 2027.
Ambasada Ibrahim Rabi’u Tahir ya yi kira ga al’ummar jihar Kano su cigaba da yin addu’a Allah ya tabbatar da nasarar takarar Sanata Barau Jibrin na Gwamna duba da yadda yake da ƙwarewa da gogewa da irin sadaukarwa da yake da ita a wakilcin al’umma da wanda yake a Majalisar Dattawa domin ƙara ciyar da jihar Kano gaba.
Ya ce Sanata Barau zai ƙara fito da sabbin hikimomi na raya ƙasa da al’ummar jihar Kano idan ya zama Gwamnan Kano da fatan Allah ya ba shi nasara zaɓen fitar da gwani da za a yi idan lokaci ya yi.
Ya kuma jinjina wa jagora Kawu Idris Hausawa bisa yadda ya jawo ‘yan Kwankwasiyya na karamar hukumar Gwale suka shiga jam’iyyar APC ƙarƙashin Sanata Barau Jibrin wannan alamu ne na nasara.
Ambasada Ibrahim Rabi’u Tahir ya ce suna ƙara mutuƙar godiya ga ɗimbin mutanen jihar Kano da suke ƙara nuna muradinsu a kan Sanata Barau I Jibrin ya fito takara Gwamnan jihar Kano a zaɓe mai zuwa.






