Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Aiki Tukuru Don Tabbatar Da Inganta Tsaro A Jihar Kano -AVM.Ibrahim Umaru

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana irin jajircewa da ƙoƙarin Gwamnan jihar Kano, Injinya Abba Kabir Yusuf ta sa ana samun kyautatuwar harkar tsaro a jihar Kano matakai da ake ɗauka na inganta tsaro ya kawo lafawar fitinun rigingimun ‘yan daba.

Kwamishinan na tsaro da ayyuka na musamman na cikin gida na jihar Kano, AVM Ibrahim Umaru mai ritaya ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai ya ce cikin ikon Allah da himma ta Gwamna Abba Kabir Yusuf da su da ake aikin da su an tashi tsaye don tabbatar da tsaron rayuka da lafiya da dukiyar al’ummar Kano.

Yayi nuni da cewa a jihar Kano babu ‘yan ta’adda amma an wayi gari an sumu sun shigo wani yanki na Shanono Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir ta tashi tsaye a kai.

Gwamna ba ya barci domin ƙoƙarin ya ga mutanen Kano sun yi barci cikin natsuwa ta ɗaukar matakin ganin an yi nasarar kawar da ‘yan ta’addan.

AVM. Ibrahim Umaru mai ritaya ya ce aikin gwamnati ne tabbatar da zaman lafiyar al’umma da kare musu rayuka da kuma dukiya, kuma Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf a kan haka yake kullum, hatta ‘yan adawa sun shaidi ƙoƙarin sa a kan inganta tsaro.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kano. AVM. Ibrahim ya yi kira ga al’ummar jihar Kano su riƙa sa Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a addu’a Allah ya cigaba da yi masa jagora a kan irin ƙoƙarin da yake na tabbatar da tsaron jama’a da gina cigaban su ta fannoni daban-daban, tare da yaba wa jami’an tsaro a kan irin ƙoƙarin da suke a kan inganta tsaro.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo