Daga Ibrahim Muhammad
An sace daya daga cikin motocinda ke yiwa Gwamnan jihar Kano rakiya ƙirar Toyota Hilux a safiyar Litinin a harabar gidan gwamnatin Kano da yanzu haka bayan an farga ake kokarin gano bincike don gano matar da barayin da suka sace ta.
Binciken ya gano cewa barayin motar sun yi dabarar shiga harabar gidan gwamnatinne da tsakar dare suka kuma fice da motar da Asuba.
Sai dai bayan faruwar lamarin, an duba na’ura watomai daukar hotuna mai matsi CCTV da ya nuna barayin sun fice ne ta babban ƙofar shiga da fita ta gidan gwamnati ba tare da wani ya tare su ba.
Sai dai akwai zargin cewa sace motar hadin baki ne wadai da suke aiki na kula da motocin wata majiya tace an Kamo direba da yake rika motar mai suna Shafi Sharp Sharp na amsa tambayoyi akan lamarin kuma babban jami’in tsaron gidan Gwamnatin na nazari kan hoto mai motsi na shige da ficen gidan.
Wata majiya daga gidan Gwamnatin jihar Kano ta ce an riga an mika bayanan motar ga jami’an tsaro domin bincike da gano inda ta shiga don kama wanda suka sace ta.







