Ayyukan Shugaban Ƙaramar Hukumar Roni A Jihar Jigawa Dr. Abba Ya’u A Shekara 1

A yayin da Dr. Abba Ya’u yake cika shekara ɗaya da ‘yan watanni a cikin office na shugaban ƙaramar hukumar Roni a jihar Jigawa, mun waiwayi waɗansu ɓangarori na ayyukan da ya yi.

ƁANGAREN ILIMI

Tun kafin Dr. Abba Ya’u ya hau kan karagar Chairman na Roni, ya kasance wanda ya kafa Gidauniyar tallafawa marassa ƙarfi, ta hanyar biyan kuɗaɗen registration ga wasu daga cikin ɗalibai ‘yan asalin ƙaramar hukumar.

Da Dr. Abba ya zama shugaban ƙaramar hukuma, sai hakan ya ƙara masa azama da jajircewa.

Bincikenmu ya tabbatar da cewa, Dr. Abba ya yi wa mutum 1238 registration, a yayin da 711 daga cikinsu kuma ya ɗauki nauyin karatunsu gaba ɗaya har su kammala. Waɗannan ɗaliban sun haɗa da waɗanda suke a Jami’a, Kwalejojin Ilimi da kuma makarantun lafiya na ciki da wajen jihar Jigawa.

ƁANGAREN RUWAN SHA

A ranar 16/12/2024 Dr. Abba Ya’u ya tunkari matsalar ruwan sha gadan-gadan yi mata kwaf-ɗaya domin magance ta.

Ya fara da gyaran babbar cibiyar da ke bai wa garin ruwa da ta daina aiki, ya sabunta ta tare da zuba sabbin kayayyaki a cikinta. A yayin da ya ya gyara sololi guda talatin da biyar (35) a mazaɓu goma sha ɗaya (II) da ke Roni.

Dr. Abba Ya’u ya bayar da gudunmawa a ɓangarori mabambanta domin ci gabantar da ƙaramar hukumar Roni gaba da suka haɗa da lafiya, tsaro, noma da tallafawa masu ƙaramin ƙarfi da ayyukan alkairi.

Yusuf Kabir ɗan Jarida/Marubuci ne, mai sharhi ne a kan al’amuran yau kullum, musamman siyasar Gabas ta Tsakiya. Yana rubutu a jaridu a ciki da wajen ƙasar nan. Za a iya samun sa kai tsaye ta wannan email ɗin: kabiruyusuf533@gmail.com

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum