Daga Ibrahim Muhammad
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta samu nasarar gano motar Toyota Hilux da aka sace a harabar gidan gwamnatin jihar da ke ofishin mataimakin Gwamna.
A rahoton da ofishin mataimakin Gwamnan ya samu daga ‘yan sanda, an gano motar ne da safiyar Laraba bayan bincike mai zurfi na haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro.
An kuma kama wanda ake zargi da satar motar, wanda aka bayyana cewa direba ne a gidan gwamnatin jihar, wanda ake zargi da sace motar na hannun ‘yan sanda yana taimakawa wajen bincike.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran mataimakin Gwamnan, Ibrahim Garba Shu’aibu ya bayyana cewa lamarin da cewa abin cin amana ne daga direban da aka kama.
Sanarwar Hukumar ‘yan sandan jihar Kano da CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya bayyana sunan Ya’u Inuwa magidanci mai shekara 50 wanda direba ne a gidan gwamnatin shi ake tuhuma da satar motar.
Rundunar yan sanda ta Kano tace an gano motar ne a unguwar ‘Yan Awaki da ke Unguwa Uku, Kano.







