Daga Ibrahim Muhammad
Gwamnanatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta kammala shiri domin ta gabatar da kasafin kuɗin na shekara ta 2026 da zai kai Naira Tiriliyan ɗaya da shi ne mafi girma a tarihin jihar.
Bayanin hakan ya fito ne a yayin taron Majalisar Zartarwa na musamman karo na biyu da aka gudanar domin tattaunawa kan ƙudirin kasafin kuɗin 2026 kafin gabatar da shi a gaban Majalisar Dokokin jihar Kano a mako mai zuwa.
Wannan na cikin sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun Gwamnan ya fitar a ranar Juma’a ga manema labarai.
Sanarwar ta yi nuni da cewa ƙarin da aka samu a ƙudirin kasafin kuɗin na da alaƙa da ƙaruwar da aka samu a kuɗaɗen shiga na cikin gida da toshe kafofin ɓarnar kuɗaɗe da gwamnatin jihar Kano take.







