Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana samar da jami’o’i masu zaman kansu da aka yi a ƙasar nan da cewa cigaba ne sosai domin gwamnati ita kaɗai a ba za ta iya gansar da kowa ba dole tana neman taimako don inganta ilimi.
Shugaban kamfanin zirga-zirga jiragen sama na Hamsly Travel and Tours Limited, Alhaji Hamisu Muhammad ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a taron yaye ɗalibai da Jami’ar SYLKINE ta Kano ta yi.
Ya ce a ƙasashen duniya haka ake domin in aka ce gwamnati ita kaɗai za ta ba da ilimi ba za ta iya wadatarwa ba, dole tana neman tallafin mutane domin a sami cigaban bunƙasa ilimi a tsakanin al’umma.
Alhaji Hamisu Muhammad shugaban Hamsly Travel and Tours Limited ya ce suna fata waɗanda suka yi saukar karatunn a Jami’ar SKYLINE karatun ya yi musu amfani su zama masu tausayi ga iyayensu musamman in akayi la’akari da irin kuɗi da suka kashe a kansu domin su yi karatun, su zama masu biyayya da tausayi ga iyayensu da sauran al’umma.
Ya yi nuni da cewa gamsuwa da Jami’ar ta SKYLINE ne ta sa ‘ya’yansa mata guda biyu na daga waɗanda aka yaye a Jami’ar saboda suna kyautata zaton za a sami tarbiyya da karatu mai inganci a Jami’ar domin asalinta daga ƙasar Dubai take tana da kula da tarbiyya da sanin ya kamata shi ne suka ga dacewar masu sa ‘ya’yansu a ciki.







