Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana ƙungiyar suluɓawa an samar da ita ne don wayar da kan dukkan Fulani na gari da maƙiyaya a kan samun ilimi na addini da na zamani da sanin muhimmancin abin da ya shafi rayuwa gaba ɗaya.
Shugaban ƙungiyar Sulluɓawa ta ƙasa Kwamared Usman Muhammad Garba ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida bayan taron da suka gudanar a Kano.
Ya ce suna kuma nusar da ‘yan’uwa makiyaya kan muhimmancin zama waje ɗaya a kan yawon ƙaura na jeji da ake da shanu yanzu ya zama yanayi ya canza, babu wuraren kiwo kuma zaman lafiya ya zama abin da ya zama, kuma dalilin wannan abin ka iya zuwa maka rasa dukiyarka ma baki ɗaya a matsayinka na Bafulatani da ba ka san wata sana’a ba wanda ya wuce kiwo.
Ya ƙara da cewa suna wayar da kan Fulani muhimmancin su sami wurare su saya su zauna wuri ɗaya a yi musu makarantu da Asibitoci da abubuwa na inganta jin daɗin rayuwa sun kuma nuna musu muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya, musamman irin wannan lokaci na dawowar shanu daga wurin na mashekari ana samun hayaniya na rashin haƙuri da kuma sakaci na barin ƙananan yara da ba su san ciwon kansu ba da shanu suna zuwa su jawowa iyayensu abin zai taɓa dukiya da rayuwa.
Ya ce sun tsayar da matsaya na cewa duk dattijo ya yi ƙoƙari ya je ya ga inda dukiyarsa take ya ga ba a bar yara ƙanana da shanu ba domin kaucewa irin waɗannan rigingimu, su kuma manoma ya yi kira gare su su zama masu adalci inda ba a taɓa musu ba, kar su ce an taɓa, kuma abin da aka taɓa da bai kai ya kawo ba a zo a yi hukunci babu cin zarafi iya ɓarnar abin da aka yi a biya ka haƙƙinka, amma bai kamata abin da bai wuce na 10,000 ba a ce sai an biya miliyan ɗaya ko 300,000, 500,000 hakan ya zama zalunci ya roƙi gwamnati da jami’an tsaro su ba da haɗin kai don magance irin wannan matsaloli.
Shugaban ƙungiyar ta sullubawa na ƙasa Kwamared Usman Muhammad Garba ya ce sun sami nasarar haɗin kan al’umma a dalilin kafa ƙungiyar da amsa kiraye-kiraye kama daga ilimi, iyaye suna sa yara a makarantu suna ma ƙirƙirar makarantun da kansu na addini da na zamani a rugage suna biya ana koyar da ‘ya’yansu ba sa jiran gwamnati.
Ya ce samu nasarar fahimtar da Fulani hukumar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro an yi su ne don kare al’umma ba an yi su bane don su cutar da su suna aiki ne don kare dukiya da rayuka, suna wayar da kai kuma Fulani suna fahimtar hakan.
Sai dai ya nuna damuwa na cewa a ɓangaren shugabanin ƙananan hukumomi ba sa samun goyon baya sosai don ya kamata sarakunan Fulani a ce duk wani abu da gwamnatin take yi ya zama ana yin sa da su, kuma duk wani tattaunawa ta tsaro ya zama ana yi da su domin su san su ma mutane kamar kowa, amma ana wofintar da su.
Ya yi nuni da cewa Fulani ne ƙashin bayan kowane irin abu na inganta cigaba a Nijeriya duk wanda ya san tarihi ya san Fulani suke da arziƙi suke taimaka wa gwamnati ba tare da gwamnati na ba su wani abu ba, suna da tamkar kamfanoni da suke ɗaukar nauyi da kansu su gudanar da abin ba tare da gwamnati tana ba su ruwan sha ko wurin kiwo ba, amma kullum suna samar da haraji ga gwamnatin da ayyukan yi gare ta.
Shugaban na Sulluɓawa na ƙasa Kwamared Usman Muhammad Garba ya yaba wa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf Fulani, ya ce babu abin da za su ce masa sai dai addu’a Allah ya sa ya gama lafiya ya sake maimaitawa karo na biyu, dukkan wani tsari da kyautatawa da jawo al’umma a jiki musamman Fulani babu abin da suka rasa iyakaci dai wakilansa da ake kusa da su suna kira gare su a ɗauki ɗabi’u irin na Gwamnan Kano, domin su taimake shi kamar yadda ya ba su amana ya sa su wakilce shi su ba su haɗin kai don gudu tare a tsira tare.







