Karamci da Mutumtaƙa: Dubban Jama’a Sun Cika Garin Kwankwaso a Ɗaurin Auren ’Ya’yan Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

Daga: Ibrahim Muhammad, Kano

Garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano ya cika maƙil da dubban jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wajenta, yayin da suka halarci ɗaurin auren ’ya’yan mashawarci na musamman ga Gwamnan jihar Kano kan harkokin siyasa, Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso.

An gudanar da ɗaurin auren ne a babban masallacin Juma’a na Kwankwaso, inda manyan baƙi na musamman suka halarta, ciki har da madugun Kwankwasiyya na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya kasance Wakilin Ango. Haka kuma mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, da shugabannin ƙananan hukumomi da dama, ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.

Jama’a da dama da suka halarci bikin sun bayyana cewa taron ya nuna irin ƙauna, karamci, tausayi da kyakkyawar mu’amala da Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso ke yi da al’umma, wanda hakan ya ƙara masa girma da daraja a idon jama’a.

Shugaban ƙaramar hukumar Ƙaraye, Haruna Safiyanu, ya ce sun zo Kwankwaso ne domin halartar auren gidan ɗan’uwa, mutum mai girmama jama’a ba tare da bambanci ba. Shi ma Alhaji Bello Musa Sumaila daga ƙaramar hukumar Sumaila ya bayyana cewa Sunusi Kwankwaso mutum ne na gaskiya, mai kyawawan halaye da soyayyar mutane.

Haka zalika, shugaban ƙaramar hukumar Sumaila ya ce ba abin mamaki ba ne ganin yawan jama’ar da suka taru, kasancewar Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso yana da himma wajen aikin jam’iyya da hidimtawa jama’a. Ya ce sun zo ne domin yi wa Amarya da Ango fatan alkhairi da roƙon Allah Ya ba su zaman lafiya da haƙuri.

Tsohon Kantoman Kumbotso, Hon. Kabiru Hussaini, ya ce taron ya nuna irin kulawa da tausayin da mashawarci na musamman ga Gwamnan Kano Sunusi Surajo Kwankwaso ke yi wa mutane, wanda ya sa manyan jami’an gwamnati da ’yan siyasa da dama suka halarta domin taya shi murna da yi wa sababbin ma’aurata addu’ar zaman lafiya.

A nasa ɓangaren, mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Ambasada Isyaku Yahaya Talba, ya ce yawan jama’ar da suka hallara ya nuna irin kyakkyawar alaƙa da Sunusi Surajo Kwankwaso ke da ita da al’umma. Haka kuma mataimakin shugaban matasan jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Mailemo, ya bayyana cewa a matsayinsu na ’yan jam’iyya sun zo ne domin taya shi murna, yana mai cewa irinsa ba a daɗe ana ganin auren da jama’a suka taru haka a tarihin Kwankwaso ba.

Shi ma mashawarci na musamman ga Gwamnan jihar Kano a ofishin mataimakin gwamna, Hon. Ɗankaka Hussaini Bebeji, ya ce yawan halartar jama’a ya bayyana irin soyayya, mutuntawa da kyakkyawar mu’amala da Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso ke yi da al’umma, wanda ya sa su ke nuna masa ƙauna da goyon baya.

Daga cikin manyan baƙi akwai Kwamishinan Ma’aikatar Kasuwanci ta jihar Kano, Shehu Wada Sagagi.

A nasa jawabin, mai masaukin baƙi kuma ubangidan auren, Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso, ya nuna matuƙar farin cikinsa da godiya ga Allah bisa samun nasarar aurar da ’ya’yansa. Ya kuma gode wa dubban jama’a da suka halarta don taya shi murna, yana mai roƙon Allah Ya saka musu da alkhairi Ya kuma ƙara zurfafa zumunci.

Haka nan ya miƙa godiya ta musamman ga jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, bisa yadda ya bar dukkan uzurorinsa ya halarci daurin auren, tare da yi masa addu’ar fatan alheri. Ya kuma gode wa mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, da tawagarsa bisa halartar taron, yana mai musu fatan komawa gida lafiya.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum