Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ƙungiyar ɗalibai guda 501 da Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya fara turawa karatu ƙasashen waje da kuma manyan jami’o’i a cikin Nijeriya, sun gudanar da taro a ranar Laraba a ɗakin taro na Jami’ar Northwest da ke Ƙofar Nasarawa, Kano.
Taron ya samu halartar tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso; Mataimakin Gwamnan jihar Kano, kuma Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo; Shugaban Kano PROPA, Hon. Habibu Saleh Mailemo; Shugaban Hukumar Ba da Tallafin Karatu, Dakta Murtala Danzaki, da kuma wasu ’yan majalisu.
Da yake jawabi a taron, Dakta Nisa’i Muhammad Gwadabe, ma’aikaci a Jami’ar Northeast Kano kuma ɗaya daga cikin ɗaliban da suka ci gajiyar shirin tura ɗalibai karatu a ƙasashen waje a zamanin gwamnatin Kwankwaso, ya bayyana cewa ƙungiyar ta shafe shekaru takwas da kafuwa.
Ya ce zuwa yanzu, sama da ɗalibai 318 ne suka halarci taron, waɗanda suka haɗa da masu digiri na farko da na biyu, baya ga masu digirin PhD da kuma waɗanda ke ci gaba da karatu a ƙasashen waje.
Dakta Nisa’i ya jaddada cewa tsarin tura ɗaliban karatu da Kwankwaso ya ƙirƙira ya kasance mai gaskiya da adalci, inda babu fifiko ko shisshigi daga jami’an gwamnati ko muƙarrabanta.
Ya ce, “Bayan miƙa takardunmu, mun jira ne kawai har sai da aka wallafa sunayenmu a jarida, ba tare da neman wata hanya ko sanayya ba.”
Ya bayyana cewa shi an tura shi ƙasar Turkiyya inda ya yi digiri na biyu. Sannan bayan dawowarsa ya samu aiki a Jami’ar Northeast Kano, wacce Sanata Kwankwaso ne ya kafa.
Ya ƙara da cewa irin wannan dama da aka ba su ya sa suke ƙoƙarin kwaikwayon jagoransu ta hanyar taimaka wa al’umma, inda suke komawa mazaɓu da unguwanninsu domin bayar da gudunmawar da za su iya, ko da kuwa ƙarama ce.
“Ba lallai sai mutum ya kai wani karatu ƙasashen waje ba. Ko siyan kayan makaranta ga marayu ko tallafa wa yara marasa karfi6 a unguwa, duk gudunmawa ce mai amfani,” in ji shi.
A ƙarshe, Dakta Nisa’i Gwadabe ya ce an yanke shawarar riƙa gudanar da taron duk shekara domin ƙara danƙon zumunci, haɗin kai da taimakekeniya a tsakanin ɗaliban da suka ci gajiyar shirin, bisa umarnin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.







