Daga Ibrahim Muhammad Kano
Zuriyar Sarkin Gini Zakariya’u ta gudanar da babban taronta na sada zumunci karo na 9 a jiya Asabar a ruffaffen ɗakin wasanni na Sani Abacha.
Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Sarkin Gini na yanzu daga tsatson zuriyar, da ya sami halartar ‘ya’ya da jikoki daga ciki da wajen jihar Kano.
Ɗaya daga cikin jikokin Sarkin Gini Muhammadu cikin wanda suka gudanar da shirya taron, Alhaji Ali Sabo Yakasai da yake zantawa da ‘yan jarida ya ce taron na sada zumunci ne kamar yadda suka saba yi a baya, amma a wannan karon sun shigo da wasu abubuwa don daɗa inganta haɗuwar zuriyar.
Ya ce idan aka dubi yadda gidan Sarkin Gini yake da tsohon tarihi a masarauta da ma jihar Kano baki ɗaya a fannin gine-gine sune sukayi yi ginin gidan Ɗanhausa da na Bimasta da gidan Makama da Birtish Council da gidan Sarki na Fanisau da na Ɗorayi duk zuriyar Sarkin gini ne suka yi.
Alhaji Ali Sabo ya ƙara da cewa wannan taron da suka yi na sabunta tafiya ne, sun samar da manhajar sadarwa na zamani da idan aka shiga zai fito da duk abin da ake nema na irin ayyukan gidan tun daga na ƙarni na 18 zuwa na 19 har zuwa na yanzu za a gani, kuma sun sabunta abubuwa kamar wajen yin zane na gini.
Ya ce har ma an ba da lambar yabo ta karramawa ga ɗaya daga cikin ‘yan zuriyar saboda ƙwarewarsa duk da ya rasu shekaru sama da 30, amma har yanzu za ka je waje a ce aikin Alhaji Baita Sarkin Gini ne, in aka je ƙasar Amurka har yanzu ayyukan da ya yi suna nan. Wannan ta sa aka karrama shi saboda sabunta al’amurra na wancan lokacin da ya yi.
Ya ce sai suka ga a wannan zamani dole su ma su sabunta abubuwa, shi ya sa suka samar da manhajar sadarwar zamani suke kuma so su haɗa su haɗa tarihin gidan da ƙungiyoyi na duniya kamar UNESCO da ke kula da abubuwa na tarihi da al’adu na duniya sun ma shigar da tarihi da ayyukan gidan Sarkin Gini ga ƙungiyoyin na duniya da ke kula da al’adu.
Ya ce yanzu a ƙasar nab suna so su sake gyara abubuwan tarihi ta tafiya da zamani, kuma suna ƙoƙarin shimfiɗa abubuwa na ƙwarewa a kan ɓangarori na gine-gine, kamar yadda a jihar Kano ake fama da samun matsalar magudanan ruwa da ke jawo ambaliya saboda irin tsare-tsaren gidaje da ake da su da hanyoyin ruwa ba a fiye ba da kula da hanyar ruwa ba.
Don haka ya yi nuni da cewa daga cikin tsarin da za su yi har da samar da ƙwararrun Injiniyoyi na ƙarami aiki da matsakaici da manya ta abin da ya shafi magudanan ruwa a Kano da ma wasu jihohi. “Wannan na daga cikin mataki da zuriyar Sarkin Gini za mu yi na sabunta sana’armu domin magance matsalolin magudanan ruwa a ƙasar nan,” in ji shi.
Alhaji Ali Sabo ya yi nuni da cewa sunan zuriyar da ta gudanar da taron shi ne Zuriyar Sarkin Gini Zakariya’u, amma ba shi ne kakan kakansu na farko ba, amma saboda daga shi zamani ya soma zuwa da ayyuka na musamman zuwan Turawa shi ya sa sunansa har yanzu yake nan, amma kafin shi akwai kakannin iyayensa da kakaninsa sun zo sun zauna kamar Sarkin Gini Sa’idu amma tarihi yana farowa ne daga Sarkin Gini Zakariya’u. Sannan sai Mahmud, sannan Muhammadu, sannan Ibrahim, sai Ahmadu, sai kuma na yanzu.
Alhaji Ali Sabo Yakasai ya ce an soma yin taron ne a baya can a SAS, amma saboda yawan zuriyar ya sa suke yin taron a manyan zauruka kamar zauren wasa na Sani Abacha domin ya wadaci kowa. Taron na bana ya sami halartar ɗimbin zuriyar da suka haɗa da ma’aikata a cikinsu da ‘yan kasuwa da waɗanda ma suka zo daga wasu jihohi da ma wajen ƙasar nan.







