Al’ummar Kano Ta Arewa Sun Yi Gangamin Neman Gwarzo Ya Fito Takarar Sanata

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Al’ummar yankin Kano ta Arewa sun gudanar da wani gangami domin nuna buƙatarsu ga Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da ya fito takarar sanatan yankin a zaɓen 2027 mai zuwa.

An bayyana cewa gangamin ya biyo bayan kiraye-kirayen da al’ummomin yankin ke yi ga tsohon ƙaramin ministan gidaje da kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, inda suke roƙon sa da ya amsa wannan kira nasu.

Shugaban kwamitin kiraye-kirayen, Hon. Magaji Shehu Lambu, wanda tsohon shugaban ma’aikata ne na tsohon ministan gidaje da raya karkara na ƙasa, ya bayyana haka ne yayin gangamin da aka gudanar a gidan Mambayya ranar Talata.

Ya ce gangamin ya samo asali ne daga yadda jama’a ke ci gaba da matsa musu a duk inda suka haɗu da su, suna roƙon a kira Gwarzo ya fito takara.

A cewarsa, kiran ya fara ne daga matakin daidaiku har zuwa ƙungiyoyi da gungu-gungun jama’a, lamarin da ya sa suka ga dacewar fito da shi fili domin duniya ta sani.

Hon. Lambu ya ƙara da cewa siyasa dama demokuraɗiyya ce, kuma kowa na da damar neman kowanne irin muƙami a Nijeriya.

Ya ce wannan ba shi ne karon farko da ake kira ga Gwarzo ya fito takara ba, domin a kalla sau uku ana yin irin wannan kira, sai dai a baya ana roƙonsa ya haƙura duk da buƙatar da jama’a ke da ita a kansa.

Ya bayyana cewa a wannan karon, al’ummar yankin na da ƙudurin ganin ya amsa kiran domin ya zama dan takara wanda za su mara wa baya ya samu nasara a zaben 2027 da yardar Allah.

Lambu ya ce al’ummar Kano ta Arewa da ma jihar Kano gaba ɗaya sun san Gwarzo a matsayin ɗan siyasa mai kishin al’umma da kyakkyawar mu’amala da jama’a, tun daga halartar bukukuwa kamar suna, aure, jana’iza, ta’aziyya da kuma duba marasa lafiya, abin da ya kara dankon zumunci tsakaninsa da al’umma.

Ya kuma yi nuni da cewa yankin na fuskantar matsaloli da dama, ciki har da lalacewar hanyar Kabuga zuwa Dayi wadda ta shafe kusan shekaru takwas ana ƙoƙarin gyaranta ba tare da samun cikakken nasara ba.

Sai dai ya ce jama’a na da kyakkyawan fata cewa idan Gwarzo ya samu dama, zai kawo sauyi, la’akari da ayyukan da ya gudanar a lokacin da yake riƙe da muƙamin minista, duk da ƙanƙanin lokacin da ya yi.

A cewarsa, daga cikin ayyukan akwai gina gidaje 500 a garin Lambu da kuma wasu 1,500 da ake ginawa a Janguza, tare da samar da kananan tituna da fitilun hasken rana da sauran ayyukan raya kasa.
Hon. Lambu ya ce gangamin ya hada mahalarta daga dukkan ƙananan hukumomin Kano ta Arewa, maza da mata, matasa da dattawa, wadanda suka bayyana aniyarsu ta marawa Gwarzo baya domin ya fito takarar sanata a zaɓen 2027.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength