Ko Makaho Ya Shafa, Zai Gane Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Yana Aiki -Hon. Gurjiya

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Jagora kuma shugaban jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Bunkure, Hon. Isma’ila Shehu Gurjiya, ya bayyana cewa ba mambobin jam’iyyarsu kaɗai ba, har ma da ‘yan adawa a jihar Kano sun gamsu da irin ayyukan da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ke yi.

Ya ƙara da cewa, “Ko mutum makaho ne, idan ya shafa a Kano zai gane cewa mai girma Gwamna yana aiki tuƙuru kuma cikin inganci, ba tare da ɗaukar bashi ba ko jinkirta biyan ‘yan kwangila ba.”

Ya kuma yi addu’ar Allah ya ƙara masa ƙarfi da ɗorewa a kan wannan tafarki na ci gaba.
Hon. Gurjiya ya ce a halin yanzu babu wata ƙaramar hukuma a jihar Kano da Gwamnan bai kai ayyukan ci gaba ba, musamman ma a yankunan karkara, kamar yadda ake gani a cikin birnin Kano.

Ya jaddada cewa shi kansa ya zagaya, kuma bai ga wata ƙaramar hukuma da ba a gudanar da ayyuka a cikinta ba.

Haka kuma, ya bayyana cewa ayyukan da Gwamnan ke yi za su amfani al’ummar jihar Kano gaba ɗaya, har ma da al’ummar da za su zo nan gaba.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar Bunkure, Hon. Aliyu Bashir Barkum (Jarman Rano), ya yaba da damar da Gwamnan ke bai wa ƙananan hukumomi wajen gudanar da muhimman ayyukan ci gaba, musamman a yankunan karkara.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength