Kasuwar Yankura GSM Plaza Na Ba Da Gudunmuwa Sosai Wajen Samar Wa Matasa Sana’o’i A Harkar Waya — Umar Boss

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Kasuwar hada-hadar wayoyin GSM ta ‘Yankura Plaza na bayar da gudunmuwa sosai wajen samar wa matasa sana’o’i a fannoni daban-daban na harkar wayar hannu.

Sabon zaɓaɓɓen shugaban Kasuwar ‘Yankura GSM Plaza, Umar Zubairu Hassan, wanda aka fi sani da Umar Boss ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya ce ya karɓi shugabancin kasuwar ne daga hannun jajirtaccen shugaban da ya gabata, Alhassan Tata, wanda ya bayar da gudunmuwa sosai wajen cigaban kasuwar, tare da assasa al’amuran alheri da suka haifar da bunƙasar kasuwar.

Umar Boss ya ce a halin yanzu matasa ne suka kai kaso 70 cikin 100 na masu harkokin kasuwanci a kasuwar, kuma hakan na taimakawa wajen hana matasa shiga ayyukan rashin tarbiyya.

Ya ce suna gode wa Allah bisa yadda matasan suka amince da tsare-tsaren da ake gudanarwa a kasuwar, lamarin da ya taimaka wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.

Ya yi nuni da cewa, yawan matasan da suke gudanar da sana’o’i a kasuwar da suka yi rijista sun kai mutum 362, baya ga masu zuwa daga wurare daban-daban domin saye da sayarwa.

Haka kuma ya tabbatar da cewa kasuwar na da cikakken tsaro sakamakon haɗin kai da take samu daga hukumomin tsaro.

Ya miƙa godiyarsa ga ofishin ‘yan sanda na Fagge da na Kasuwar Sabon Gari, da sauran hukumomin tsaro da suke ba su gudunmuwa wajen tabbatar da tsaro a kasuwar.

Umar Boss ya ce a kasuwarsu ta ‘Yankura GSM Plaza suna ɗaukar matakai masu tsauri domin tabbatar da cewa duk wayar da za a kawo kasuwar domin sayarwa ba ta haramtacciyar hanya aka samo ta ba.

Ya ce suna da hanyoyi daban-daban na bincike da tantancewa domin tabbatar da gaskiyar wanda ya kawo wayar sayarwa.

Ya ƙara da cewa duk wanda aka kama da wayar sata ko wadda ba ta halastacciyar hanya aka samu ba, sukan miƙa shi ga hukumomin tsaro.

Haka kuma sukan ɗauki hoton wanda aka kama da irin wannan laifi su liƙa a allon sanarwa na ofishin kasuwar.

Bugu da ƙari, ya ce sukan yi ƙoƙarin nemo ainihin mamallakin wayar domin mayar masa da haƙƙinsa, kuma mutane da dama suna zuwa suna nuna godiyarsu bisa wannan aiki.

Umar Boss ya gode wa Allah da cewa matsaloli a kasuwar ba su da yawa, domin mafi yawan masu mu’amala a kasuwar sun san abin da ya kamata su yi, kuma suna bai wa shugabannin kasuwar cikakken haɗin kai.

Ya kuma ce sakamakon yadda akwai matasa da dama a ‘Yankura GSM Plaza da ke ƙoƙarin neman na kansu, amma ba su da isasshen jari, suna fatan gwamnati za ta duba halin da suke ciki ta tallafa musu.

Ya bayyana cewa a baya an tattara sunayen wasu matasa a kasuwar tare da yi musu alƙawarin za a tallafa musu da jari domin gudanar da sana’o’in POS da sayar da kayan waya, don haka suna roƙon gwamnati da ta cika wannan alƙawari domin ƙarfafa musu sana’o’insu.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum