Daga Zubairu Lawal
Ahmed Wadada, Sanata (APC, Nasarawa West) ya gargadi magoya bayansa da su guji kalamai marasa tsari da kuma ra’ayoyin da ke haifar da rarrabuwar kai, gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar domin babban zaben 2027.
Hon. Wadada ya yi wannan kira ne a wani taron manema labarai a ranar Lahadi a zauren NUJ dake garin Lafia.
cikin makon da ya gabatane Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana Wadada a matsayin wanda yake so ya gajeshi a matsayin gwamna, tare da bukatar shugabannin jam’iyya da magoya baya su tabbatar ya samu tikitin APC domin zaben 2027.
Sanatan ya gargadi magoya bayansa da kada su kai hari ko miyagun maganganu ga sauran masu neman takara, ko magoya bayansu ko shugabannin jam’iyya, ta hanyar amfani da karfi, kafafen yada labarai ko shafukan sada zumunta saboda sabanin ra’ayoyin siyasa.
Ya jaddada cewa yakin niman zabe dole ne ya kasance bisa tunani da manufofi, ba tare da cin mutunci ba, yana mai kira ga masu ruwa da tsaki su wuce tunanin bambance-bambancen kabila ko addini.
“Na roki dukkan magoya bayana a fadin Jihar Nasarawa da su guji kalamai marasa tsari da ka iya tayar da hankalin jama’a.
“Bai kamata mu yi kamfen bisa addini, kabila ko kai hare-haren mutum ba.
Mu mai da hankali kan manufofi, kwarewa da makomar jiharmu,” in ji shi.
Ahmad Wadada ya bayyana cewa jihar ta samu ci gaba a karkashin gwamnatocin baya, ciki har da na Abdullahi Adamu, Aliyu Akwe-Doma, Umaru Al-Makura da kuma gwamnan da ke kan karagar mulki a yanzu, Abdullahi Sule.
Ya ce dorewar irin wannan ci gaba na bukatar kwarewa da kuma kyakkyawan halayya daga ‘yan siyasa.
Sanata Wadada ya yi alkawarin cewa yakin niman zabe, idan aka sanar da shi a hukumance, zai mayar da hankali kan tarihin aikinsa na majalisa tare da bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi ga matasa, noma da tsaro.
Ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule kan jagorancinsa, tare da sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar APC, yana mai nuna muhimmancin hadin kai a cikin jam’iyyar kafin zaben.
Ahmad Wadada ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin addini da kafafen yada labarai, musamman Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), da su inganta zaman lafiya da wayar da kan al’umman Jihar.
Ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin jam’iyya, masu neman takara, magoya baya da al’umma gaba daya, da su fifita muradun jihar gaba daya fiye da na kashin kai ko na bangare.







