Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jigo a jam’iyyar APC kuma ɗaya daga cikin hadiman tafiyar siyasar Hon. Hassan Shehu Hussain, ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Muhammad Adamu Bomboy, ya bayyana samun tikitin takara ba tare da hamayya ba da Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi a matsayin alamar gamsuwar al’umma da salon mulkinsa cikin shekaru uku da suka gabata.
Bomboy ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce al’ummar jihar sun shaida irin muhimman ayyukan da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta aiwatar a fannoni daban-daban tun bayan hawansa mulki.
Ya ce gwamnatin ta mayar da hankali wajen bunƙasa ilimi, inganta harkokin lafiya, gina da gyaran hanyoyi a birane da karkara, ƙarfafa tsaro, samar da ruwan sha mai tsafta da kuma aiwatar da shirye-shiryen da suka taimaka wajen kyautata rayuwar al’umma.
“Irin ayyukan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aiwatar cikin shekaru uku sun sanya al’ummar Kano ci gaba da nuna goyon baya gare shi. Wannan ne ya sa ya samu tikitin takara ba tare da hamayya ba, wanda ke nuna amincewa da jagorancinsa,” in ji Bomboy.
Dangane da ƙaramar hukumar Nasarawa, Bomboy ya ce sake tabbatar da Hon. Hassan Shehu Hussain a matsayin ɗan takarar APC na majalisar wakilai ta tarayya ya samo asali ne daga irin ayyukan ci gaba da ya aiwatar a mazabarsa.
Ya ce baya ga gabatar da ƙudiri da dokokin da suka amfani al’umma a matakin ƙasa, ɗan majalisar ya gudanar da ayyukan raya ƙasa da suka haɗa da gina asibitoci, samar da hanyoyi, gina makarantun zamani da na addini, da kuma tallafa wa matasa, mata da iyalai da jari domin dogaro da kai.
Haka kuma, ya ce an raba wa al’umma babura, motoci da sauran kayayyakin tallafi domin rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙi da inganta rayuwar jama’a.
Bomboy ya bayyana cewa shekaru uku na mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma wakilcin Hon. Hassan Shehu Hussain sun kasance abin alfahari ga al’ummar Jihar Kano da musamman mazauna ƙaramar hukumar Nasarawa.
Ya ƙara da cewa al’ummar yankin na ci gaba da amfana da ayyukan ci gaba da shugabannin biyu ke aiwatarwa, lamarin da ya ce zai ƙara musu karɓuwa a idon jama’a.
“Saboda irin ayyukan alheri da suka aiwatar da kuma ribar da al’umma ke ci gaba da samu, muna da yakinin cewa a zaɓen shekarar 2027 jama’a za su sake ba su goyon baya domin ci gaba da ayyukan ci gaba,” in ji shi.






