Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Gidauniyar NNPCL, reshen ayyukan jin ƙai na NNPC Ltd, ta ƙaddamar da sabuwar na’urar binciken cututtuka ta zamani mai ƙarfin 1.5 Tesla MRI Scan da aka girka a Asibitin Kashi na Ƙasa da ke Dala, Kano, domin inganta binciken cututtuka cikin sauri da sahihanci.

An bayyana cewa tallafin na daga cikin ƙoƙarin kamfanin na bunƙasa harkokin lafiya da sauƙaƙa ayyukan likitanci a faɗin Najeriya. Ana sa ran na’urar za ta taimaka wajen gano da kuma kula da cututtukan da suka shafi ƙashi, ƙwaƙwalwa, tsokoki, raunuka da kuma wasu matsalolin lafiyar mata.

Da take jawabi a wajen bikin ƙaddamar da na’urar da aka gudanar a ranar Alhamis, Babbar Daraktar Gidauniyar NNPCL, Mrs Emmanuella Arukwe, wadda ta wakilci Babban Daraktan NNPC Ltd, ta ce tallafin na cikin manufar kamfanin ta bayar da gudummawa mai ɗorewa wajen bunƙasa harkar lafiya a ƙasar nan.

Ta ce kamfanin na da burin tabbatar da cewa zuba jarin da yake yi a ayyukan jin ƙai yana haifar da sauyi mai ma’ana da kuma amfanar al’ummomin da yake yi wa hidima.

Ita ma Darakta Zartarwa ta Gidauniyar NNPCL, Mrs Rose Okonkwo, wadda ta wakilci Mataimakin Shugaban NNPC Ltd, ta ce kamfanin ya wuce aikin hako mai kawai, inda yake taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar ’yan Nijeriya.

A cewarta, ƙaddamar da na’urar MRI a Asibitin Ƙashi na Dala wata shaida ce ta ƙudirin NNPC Ltd na samar da ci gaba mai ɗorewa, musamman a fannin lafiya, domin amfanin al’ummomin da ke da ƙarancin damar samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.

Ta ƙara da cewa na’urar za ta taimaka wajen ƙarfafa ayyukan lafiya ga al’ummar Kano da yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya, da kuma sauran marasa lafiya da ke neman kulawa a asibitin.

A nasa jawabin, Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Alhaji Abubakar Labaran Yusuf, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Gidauniyar NNPCL bisa wannan tallafi, wanda ya bayyana a matsayin wani gagarumin ci gaba wajen inganta ayyukan gano cututtuka da kuma samar da magani cikin lokaci.

Shi ma Shugaban Asibitin Ƙashi na Dala, Dr. Isa Nurudeen, ya gode wa NNPC Ltd kan tallafin, yana mai cewa zai taimaka matuƙa wajen inganta ayyukan asibitin da kuma hidimomin da yake bayarwa ga marasa lafiya.

Bikin ya samu halartar manyan jami’an NNPCL, ma’aikatan asibitin, jami’an gwamnati, likitoci, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a harkar lafiya.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum