Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jam’iyyar NDC ta tabbatar da Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takararta na gwamnan Jihar Kano, yayin da ta zaɓi Mustapha Rabi’u Kwankwaso a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamna domin fafatawa a babban zaɓen shekarar 2027.
Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun bayyana cewa haɗakar Aminu Gwarzo da Mustapha Kwankwaso wani muhimmin mataki ne na siyasa da aka ɗauka domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma faɗaɗa tasirinta a sassa daban-daban na Jihar Kano.
A cewarsu, zaɓen waɗannan ’yan takara biyu ya yi daidai da ra’ayin mafi yawan magoya bayan jam’iyyar, tare da nuna aniyar NDC na gina ƙungiya mai ƙarfi wadda za ta iya fafatawa da sauran jam’iyyu a zaɓen 2027.
Sun kuma bayyana cewa jam’iyyar na da yakinin cewa haɗin gwiwar Gwarzo da Mustapha Kwankwaso zai taimaka wajen jawo ƙarin goyon bayan al’umma tare da ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a fagen siyasar Kano.
Jam’iyyar ta ce tana sa ran wannan tsari zai taimaka mata wajen cimma burinta na lashe zaɓen gwamnan Jihar Kano a shekarar 2027.






