Kano Ta Karɓi Baƙuncin Wasan Tseren Dawakai Na ‘Renewed Hope’

Daga Ibrahim Muhammad Kano.

An bayyana ba za a cika tarihin tseren dawakai a ko’ina a Najeriya ba, ba tare da an sanya Kano ba, domin ta na da matuƙar tarihi a harkar koodineta na Ƙasa na Hukumar Tseren Dawakai ta Najeriya, Alhaji Mustapha Abubakar Bidda ne ya bayyana hakan da yake jawabi a wurin buɗe gasar tseren dawakai a Kano mai taken “Renewed Hope a Kano ranar Laraba
Bidda wanda ke da sarautun gargajiya na Sarkin Dawakin Nupe da Sarkin Sukuwar Ƙasar Hausa ya bayyana Kano a matsayin “gari mai tarihi ƙwarai” a harkar teren Dawaki.

“Ina tuna wannan fili na sukuwa an gina shi tun zamanin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Audu Bako. Tun daga lokacinsa har zuwa yanzu, tseren dawakai na gudana a Kano tsawon lokaci,” in ji Bidda.

Ya ce Kano ta kasance birni na fitattun masu dawakai kuma an yi tseren da ba su da adadi a ciki. “A matsayinmu na hukumar da ke kula da harkokin tsere a Najeriya, tarihi ba zai taɓa mantawa da mu ba wajen mayar da Kano ɗaya daga cikin fitattun wurarenmu na tsere.”

Bidda ya ce gasar tseren Dawaki na Renewed Hope zai gudana daga ranar Laraba, 25 ga Yuni zuwa 28 ga Yuni. Ana sa ran za a yi tsere 20 daga sassa daban-daban, wanda zai fara da dawakai na yankin Arewa da kuma na Najeriya waɗanda hukumar ke ƙarfafawa kuma ake samarwa a cikin kasa.

“Wannan sukuwa zai zama wani babban taro na musamman. Tsere ne na musamman da ba a taɓa ganin irinsa a Kano ba,” ya ƙara da cewa.

Babban abin da ya sa wannan gasar ta zama ta musamman a bana shi ne fara amfani da “starting gate” wacce ka’ida ce ta duniya a tseren dawakai.

Ɗaya ne daga cikin muhimman abubuwan da ke faruwa a tseren nan na Kano, wanda ya fara a Najeriya.ne a wannan shekara, shi ne “starting gate. Ba a taɓa yin hakan a Najeriya ba ,” in ji Bidda. “Kano ce wuri na uku da za a fara amfani da starting gate wajen fara tseren dawakai.” hakan na nuna cewa Najeriya ta kai matakin shiga gasa ta duniya.

Starting gate na nufin duk dawakai za su fara tashi a lokaci guda. Wannan yana nuna adalci kuma ya yi daidai da ƙa’idar duniya. Yanzu ana iya kimanta tserenmu kamar kowane tsere a duniya.”

Tun da aka fara tseren dawakai a Najeriya a 1962, wannan ne karo na farko da za a yi amfani da starting gate. “Najeriya na ci gaba. Muna ƙara zama sanannu a cikin gida da wajen ƙasa, kuma wannan tseren yana da masu kallo daga sassan duniya,” in ji Bidda.

A cewar hukumar, akwai kyaututtukan kuɗi da suka kai kusan Naira miliyan 50 da sabbin motoci 7 da za a ci a gasar.

“Waɗannan ƙananan kyaututtuka ne kawai don godiya da ƙarfafa mutane su shiga harkar tseren dawaki. In ba haka ba, kyaututtukan ba za su kai kuɗin da ake kashewa wajen kula da dawaki ba. Don ƙarfafawa ne kawai,” in ji Bidda.

Gasar tseren dawakai na Renewed Hope a Kano ya fara ranar Laraba da yamma, inda aka riga aka lashe kofuna da dama. Taron zai ɗauki kwanaki uku.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum