An Buɗe Taron “Indonesia-Kano Expo 2026” Karo Na 3 A Kano Da (KASCOTE) Ta Shirya

Daga Ibrahim Muhammad, Kano.

A ranar Alhamis ne aka buɗe taron “Indonesia-Kano Expo 2026” karo na uku a jihar Kano, wanda ƙungiyar KASCOTE ta shirya.

Shugaban ƙungiyar KASCOTE, Alhaji Hassan Yaro, wanda ya shirya taron nuna kasuwanci tsakanin Indonesia da Kano, ya yaba da yadda mutane suka amsa kiran halartar taron.

Ya ce sun samu halartar wakilan yan kasuwa daga ƙasar Indonesia karkashin jagorancin Jakadan Indonesia a Najeriya, Mista Bambang Suharto. Haka kuma akwai tawagar yan kasuwa daga ƙasashe bakwai daban-daban na Afirka. An yi tattaunawa mai zurfi kan harkokin kasuwanci.

Alhaji Hassan Yaro ya ce abin farin cikinsu a wannan karo shi ne samun karin jami’o’i daga Indonesia. Ya bayyana cewa hakan ya samu ne sakamakon nasarar alakar kasuwanci da aka kulla.

“Saboda haka muna ba wa matasanmu damar samun ilimi mai kyau, da kuma samun tallafin scholarship wajen karatun su,” in ji shi.

Ya ce tun daga lokacin da aka fara gudanar da taron a Kano shekaru uku da suka gabata, ya samar da tasiri mai girma. Ya ba da misali da yadda dan kasuwan Indonesia da bai taba zuwa Afirka ba, ya zo Kano, ya ga abubuwa, ya kuma samu abokan kasuwanci. Haka ma dan Kano da bai taba zuwa wata ƙasa ba, ya hadu da abokan hulda, aka kulla alaka.Yan kasuwa Maza da mata sun samu abin farin ciki da fa’ida a cikin hakan.

“Kokarinmu shi ne mu kai wanda bai sani ba inda ya kamata ya sani. Muna jawo mutane mu hada su da masu yan kasuwa , mu nuna musu abin da ba su sani ba, domin su inganta kasuwancinsu,” in ji shi.

Alhaji Hassan Yaro ya ce nan gaba za su ziyarci ƙasashe irin su Turkiyya, Faransa, Jamus, da Spain, duk don harkokin kasuwanci. Daga nan kuma za su je China, su dawo gida cikin wannan shekarar. Ya kara da cewa akwai shirin gudanar da irin wannan taron da yan ƙasar Vietnam ma.

Ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano bisa tura Kwamishinan Kudi zuwa taron. Ya ce suna fatan a cikin watan Oktoba, akalla yan kasuwa sama da 150 za su je Indonesia, kuma yana fatan Gwamna Abba Kabir Yusuf zai samu damar ya jagorance su a tafiyar.

Shugaban Cibiyar Masana’antu, Kasuwanci da Noma na Jihar Kano, Ambasada Hamza Usman Darma,shima a yayin taron ya bayyana taron a matsayin mai cike da ci gaba. Ya ce an samu halartar wakilai daga Indonesia da kuma kamfanoni na cikin gida.

Ya yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da damar da kamfanonin da suka zo daga Indonesia da sauran wurare suka kawo, domin cigaban masana’antu a Kano da Najeriya baki daya.

“Cibiyar Kasuwanci ta Kano tana da kyakkyawar alaka da ƙungiyoyi, musamman KASCOTE da ta shirya wannan taron. Muna mara mata baya domin samun nasara. Duk wata ƙungiya da ke da wani abu da zai taimaki wannan ƙasa, muna shirye mu mara mata baya domin cigaban Kano da Najeriya,” in ji Darma.

Taron ya samu halartar Kwamishinan Kudi na Jihar Kano Dan maraya da Damadamin Kano wanda ya wakilci Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi II, Jakadan Indonesia a Najeriya, Mista Bambang Suharto, da sauran yan kasuwa daga ciki da wajen ƙasar.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum