Daga Ibrahim Muhammad Kano
Shugaban Ƙaramar Hukumar Dala, Hon. Surajo Imam, ya yaba da irin ƙoƙarin fitaccen ɗan kasuwar gasasshen naman rago, Alhaji Malami mai nama bisa yadda yake buɗe wuraren sayar da nama na zamani da kuma samar wa matasa ayyukan yi.
Ya bayyana hakan ne a wajen buɗe wani sabon katafaren wajen sayar da gasasshen naman rago da ke kan Titin Ibrahim Taiwo a ranar Talata.
Hon. Surajo Imam ya ce kasuwanci na ci gaba da bunƙasa a jihar Kano, kuma Alhaji Malami ya fara ne daga tallan nama a kwano, har ya kai ga samun matsuguni a Sansanin Alhazai. Bayan haka ya ƙara buɗe wasu wurare a sassa daban-daban na jihar Kano, har zuwa yanzu da ya buɗe na tara.
“Ko ba komai, ta yadda yake samar wa matasa aiki a wajen sayar da namansa, yana taimaka wa gwamnati wajen rage zaman banza musamman yanzu. Sana’ar fawa ba ta tsaya ga wanda ya gada ba, kowa na iya shiga. Har da Fulani yanzu suna yi. Wannan dama ce da arziƙi ya ƙara bunƙasa a Kano,” in ji shi.
Shugaban ya ƙara da cewa nasarar da Alhaji Malami ya samu na da alaƙa da irin biyayya da kyautatawa da yake yi wa iyayensa. “Duk wanda ya biyayya ga iyaye zai samu nasara a rayuwarsa, domin Allah ne ya ce a yi musu biyayya,” ya ce.
A nasa jawabin na godiya, Shugaban wajen sayar da naman na Malami, Alhaji Malami “Hajj Camp” ya bayyana godiya ga al’ummar Kano bisa karamcin da suke yi na ɗaukar ɗansu da baƙi ba tare da bambanci ba.
Ya kuma yaba da ƙoƙarin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kulawa da yake ba wa bunƙasar kasuwanci da kuma turo da wakilci da yake yi a dukkan tarukansu.
Alhaji Malami mai nama ya yi kira ga matasa da su jajirce. Ya ce shi ya shafe sama da shekaru 35 a Kano, tun zamanin mulkin Ibrahim Babangida yana tallan nama. Yana shiga kasuwannin Singer, Kantin Kwari, Sabon Gari, Ujule da Kasuwar Sansanin Alhazai har Allah ya ba shi damar kafa nasa wajen.
“Amma matasa ba sa iya tsayawa su jajirce su nemi kuɗi sai suna tunanin su samu kaya mai kyau ko mota nan take. Wannan ba ya samuwa sai da aiki tuƙuru, dauriya, gaskiya, riƙon amana da biyayya ga iyaye,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, ɗaya daga cikin abokan Alhaji Malami, Alhaji Abdu ‘Yandoma ya ce Malami mutumin kirki ne mai kyautata wa al’umma. Ya ce yanzu Malami yana da ma’aikata sama da 100, kuma duk wanda ya yi mu’amala da shi zai ji daɗinsa saboda ba ya cin amana.
“Alhaji Malami yana kula da ‘yan’uwa, abokai da mabuƙata. Yana tsayawa kan gaskiya kuma yana ƙarfafa mana gwiwa. Hatta ma’aikatan gwamnati ba lallai ne su samu albashin da yake biya ba,” in ji Alhaji Abdu ‘Yandoma.
Manyan ‘yan kasuwa, jami’an gwamnati da jami’an tsaro daga ɓangarorin daban-daban ne suka halarci taron buɗe sabon katafaren wajen sayar da gasasshen naman na Alhaji Malami mai nama da ke kan Titin Ibrahim Taiwo.







