YEIDEP: Muna Sa Ran Samun Karɓuwa Sosai a Yobe — Hassan Kaku

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Mai Kula da Shirin YEIDEP’s Financial Partners na Jihar Yobe, Hon. Hassan Kaku Hassan, ya bayyana cewa suna sa ran shirin zai samu karɓuwa sosai a tsakanin matasan jihar.

Ya ce babban burin shirin shi ne taimaka wa matasa su samu sana’o’i da hanyoyin dogaro da su kansu, domin rage rashin aikin yi da kuma hana su faɗawa cikin munanan halaye.

Hon. Hassan ya bayyana hakan ne yayin taron ƙaddamar da shirin a Jihar Kano, inda ya ce shirin zai samar da tallafi kai tsaye ga waɗanda suka cika sharuɗɗan cin gajiyarsa.

Ya ce duk wanda ya buɗe asusun banki kuma aka shigar da bayanansa cikin tsarin, tallafin da aka ware masa zai shiga asusunsa kai tsaye. “Duk wanda ya buɗe asusun ajiya na banki kuma aka saka lambar sa cikin tsarin, duk lokacin da aka bayar da tallafi, zai shiga cikin asusunsa kai tsaye,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa shirin zai kuma ba matasa horo kan sana’o’i daban-daban domin su samu damar dogaro da kansu.

A cewarsa, rashin ilimi da rashin aikin yi na daga cikin abubuwan da ke jefa wasu matasa cikin shaye-shaye da sauran munanan ayyuka.

Hon. Hassan ya ce za su ci gaba da wayar da kan matasan Yobe kan muhimmancin shirin da kuma hanyoyin da za su bi domin cin gajiyarsa. Ya ce suna da kyakkyawan fata cewa shirin zai samu karɓuwa sosai a jihar.

A ƙarshe, ya yaba da yadda shirin ke gudana a Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Shugaban Shirin na Arewa, Hon. Sani Musa Danja, Mai Ba Gwamnan Kano Shawara kan Harkokin Matasa da Wasanni, bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ganin shirin ya yi nasara.

Ya kuma yi kira ga waɗanda za su amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata, domin ya amfani kansu, ’yan uwansu, makwabta da kuma al’umma baki ɗaya.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo