Hon. Kabiru Dahiru Sule, wanda aka fi sani da ADS, ya zama ɗaya daga cikin fitattun muryoyin siyasa a Ƙaramar Hukumar Tarauni ta Jihar Kano, inda ya gina matsayinsa na siyasa bisa wakilcin al’umma, fafutukar ganin an inganta rayuwar jama’a ta fuskar dokoki da kuma ayyukan ci gaban al’umma.
A matsayinsa na wakilin Alumma a zauren majalisar dokokin ta jiha dayake wakiltar karamar Tarauni ADS ya mayar da hankali wajen gudanar da siyasar da ta shafi bukatu da muradun al’ummar da yake wakilta.

Ayyukansa daya aiwatar sun hada da na kyakkyawar mu’amala da al’umma da suka shafi fannoni daban-daban na ci gaba, ciki har da kiwon lafiya, ilimi, samar da ababen more rayuwa da kuma tallafawa matasa.
Shirye-shiryensa da ayyukansa na majalisa sun ci gaba da jawo hankalin mazauna Tarauni da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa.
Baya ga ayyukansa a Majalisar Dokoki, ADS ya ci gaba da kasancewa cikin al’umma, inda yake hulɗa da shugabannin al’umma, matasa, ƙwararru, ’yan kasuwa da sauran ƙungiyoyi daban-daban a faɗin mazabar. Wannan hulɗa ta taimaka wajen ƙarfafa alaƙarsa da jama’a tare da ƙara masa suna a matsayin wakilin da ke da kusanci da waɗanda yake wakilta.
Magoya bayansa na bayyana shi a matsayin ɗan siyasar da ya mayar da hankali kan ci gaba mai amfani kai tsaye ga al’umma, musamman a fannonin kiwon lafiya, ilimi, hanyoyi da sauran muhimman ayyukan more rayuwa.

Wadannan fannoni sun zama wani muhimmin ɓangare na irin salon siyasar da ADS ya gina.
Masu sa ido kan harkokin siyasa kuma na kallon ADS a matsayin ɗaya daga cikin sabbin ’yan siyasar Tarauni da ke ƙoƙarin haɗa a wakilcin majalisa da kuma kasancewa kusa da jama’a a matakin ƙasa.
Ƙaruwar tasirinsa ta sanya ya zama ɗaya daga cikin fitattun mutane da ake la’akari da su yayin tattaunawa kan makomar siyasar karamar hukumar Tarauni.
Yayin da shirye-shirye da sabbin ƙawance na siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027 ke ci gaba da ɗaukar hankali, tarihin ayyukan ADS a Majalisar Dokokin Jihar Kano da kuma ci gaba da hulɗarsa da al’ummar Tarauni na iya kasancewa muhimmin batu a tattaunawar da za a yi kan shugabanci, wakilci da ci gaban al’umma.

Ga wasu daga cikin mazauna karamar hukumar Tarauni, tafiyar ADS a harkokin siyasa na wakiltar wani sabon babi a tarihin dimokuraɗiyyar yankin babi da ke nuna cewa ingantaccen wakilci, kusanci da jama’a da kuma shugabanci mai mayar da hankali kan ci gaban al’umma na daga cikin manyan abubuwan da jama’a ke sa ran samu daga shugabanninsu.
AYYUKAN 2023
NASARORIN HON. (ADS) DAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KANO A KARAMAR HUKUMAR TARAUNI
SHIRIN KARARFAFA MATASA DA JAM’A’A NA 2023
1. Rarraba Babura ga matasan Tarauni mai darajar kudinsu ya kai Naira Miliyan 7.
2. Bayar da tallafin kudi Naira 1,000,000 ga mambobin Zartarwa na NNPP na Karamar Hukuma.
3. Bayar da tallafin kudi Naira Miliyan 3.5 ga mambobin Zartarwa na mazabu.
4. Bayar da tallafin kudin hannu Naira Miliyan 2.5 ga mambobi 50 na Ƙungiyar Nakasassu ta Tarauni.
5. Rarraba Injin yin taliya 150 tare da kilogiram 10 na fulawa i ga matan Mazabar Tarauni.
6. Jimillar darajar tallafin ga mata: Naira Miliyan 3.
SHIRIN KARARFAFA MATASA DA JAM’A’A NA 2024
1. Raba Babura 25 ga matasan Tarauni na kimar Naira Miliyan 25.
2. Rarraba Kekunan dinki 50 ga mata 50 a Tarauni na kimanin Naira Miliyan 7.5.

3. Rarraba Injin POS da tallafin Naira 50,000 ga matasa 50 na Tarauni na kimanin Naira Miliyan 4.
4. Rarraba tallafin kudi Naira Miliyan 8.5 ga wakilai 425 na Karamar hukumar Tarauni.
5. Rarraba tallafin kudi Naira Miliyan 3.5 ga mambobin Zartarwa 140 na mazabu a Karamar hukuma Tarauni.
6. Rarraba tallafin kudi Naira 200,000 ga ƙungiyoyin siyasa 10 a Tarauni jimilla Naira Miliyan 2.
7. Horar da matasa Maza da mata 250 na Tarauni kan sana’o’i daban-daban.
AYYUKAN CI GABAN KIYON LAFIYA NA ADS
1. Ingantawa / Gina Asibitin Kula da lafiya a matakin Farko a (PHC) a Tarauni.
2. Gina Cibiyar Lafiya ta Ja’oji Gyadi-Gyadi Arewa.
3. Gina Asibitin Kula da lafiya a matakin Farko na ADS Hotoro Danmarke.
4. Gina Dakin Haihuwa da Tandas a Gyadi-Gyadi Kudu PHC.
5. Inganta Ja’oji (PHC) zuwa Cibiyar Lafiya ta mai aiki awa 24.
6. Inganta Gyadi-Gyadi Kudu (PHC) zuwa aiki awa 24.
7. Aikin Kula da Ido Kyauta ga marasa lafiya 2,000 a Tarauni.
8. Hidimar Lafiya ta Kyauta ga marasa lafiya 1,000 a Hausawa (PHC) a watan Oktoba, 2023.
9. Hidimar Lafiya Kyauta ga marasa lafiya 1,000 a Ja’oji (PHC) a 2023.

10. Hidimar Lafiya ta Kyauta ga marasa lafiya 1,000 a Unguwa Uku (PHC) a Oktoba 2023.
11. Hidimar Lafiya Kyauta ga marasa lafiya 1,000 a Tarauni (PHC) a Oktoba, 2023.
12. Gudanar da Kula da Lafiya Kyauta a Asibitin matakin Farko na ADS a Danmarke a Fabrairu, 2024.
13. Rarraba Katin Marasa lafiya 30,000 ga Asibitoci 10 na matakin Farko a Tarauni a Disamba, 2023.
14. Biyan Kudin Jinya ciki har da tiyata da kulawa ta musamman ga marasa lafiya 50 wanda ya kai sama da Naira Miliyan 8.
15. Sabunta Asibitin Kula da lafiya a matakin Farko na Daurawa.
16. Daukar nauyin Kula da lafiyar Hakora a Asibitin matakin Farko a Kauyen Aluga marasa lafiya 1000.
WASU KARIN AYUKAN 2026
A BANGAREN LAFIYA, ILIMI DA GABATAR DA KUDURORI DA ADS YA YI
1. Ginin asibiti unguwar gano.
2. Ginin asibitin yara a kauyen alu.

3. Bada kullawa na lafiya da rabon magani kyauta a asibitin jaoji na mutum 1,000.
4. Gyara da inganta asibitin Daurawa.
5. Bada kula na hakori a asibitin shargalle dake kuyen alu na mutum 1,000.
BANGAREN ILIMI 2026
1. Gyaran makaranta GSS Gyadi gyadi kudu.
2. Gina makaranta imam malik a mazabar daurawa.
3. Gina makaranta GASS babban giji.
BANGAREN KUDIRI
1. Kudirin titi Foundation road mazabar tarauni.
2. Kudirin titi dan tsinke.
3. Kudirin titin maraba maradi mazabar hotoro.
4. Kudirin titin yan awaki zuwa zaria road.
NASARORIN A MAJALISA DA GABATAR DA KUDURORI
Kudiri na ɗaukaka Asibitin Kula da lafiya na matakin Farko na Tarauni zuwa matsayin Babban Asibiti a Ƙaramar Hukumar Tarauni.
Kudiri ga Gwamnatin Jihar kan sake gina Titin Kasuwar Tarauni a Ƙaramar Hukumar Tarauni.
Kudiri ga Gwamnatin Jihar kan gina magudanar ruwa daga Gidan Gwamnatin kano zuwa Gidan man Aliko a Ƙaramar Hukumar Tarauni.
Kudiri- Ga Gwamnatin Jihar kan gina hanya daga Masallacin Bilal zuwa Hassan Ibrahim Gwarzo a Ƙaramar Hukumar Tarauni.
Kudiri ga Gwamnatin Jihar kan yi wa Kabarin Dantsinke shinge saboda sace gawarwaki, da yi wa dukkan kaburbura a Jihar Kano shinge.
Daftarin Doka. Gabatar da “Daftarin Dokar Hukumar Kyautata Birane da Tsara Muhalli ta Jihar Kano, 2024”.
Kudiri na Haɗin Gwiwa ga Gwamnatin Jihar kan gina hanya daga Ungogo zuwa Minjibir duka a Ƙananan Hukumomin Ungogo da Minjibir.

Tallafawa Kudiri Ga Gwamnatin Jihar kan gina hanya daga Lajawa – Rimi ‘Yan Alewa – Sogame ‘Yandaji – Makera – Tandawa – Dadin Kowa Boka zuwa Ajingi Duk a Ƙaramar Hukumar Wudil.
Tallafawa Kudiri ga Gwamnatin Jihar kan ɗaukaka Asibitin Ajingi “Town Cottage zuwa matsayin Babban Asibiti a Ƙaramar Hukumar Aginji.
Tallafawa Kudiri ga Gwamnatin Jihar kan sake gina Hanyar Minjibir – Chedi – Yola – Ladin Dandake – Zango – Sarbi – Kongo duka Ƙaramar Hukumar Minjibir.
Mai Tallafawa Kudiri ga Gwamnatin Jihar kan kammala aikin da ke gudana daga Garin Ali – Dal da gina gada a Mazabar Maidaa Gurjiya duka a Ƙaramar Hukumar Garko.
AYYUKAN CIGABAN HARKAR ILIMI NA ADS
1. Gina Sabon rukunin ajiujuwa na Kwankwasiyya a Makarantar Firamare ta Dantsinke, Darmanawa.
2. Gina Tandas na VIP masu ɗaki 4 a Cibiyar Mata ta Unguwa Uku.
3. Gina Inuwar Tsangaya a Cibiyar Mata ta Unguwa Uku.
4. Sabunta Gina na Makarantar Firamare a Hausawa Model Primary School.
5. Rarraba Littafai da kayan motsa jiki 20,000 da rajista 5,000 ga Makarantun Firamare 10 na Tarauni.
6. Gina Kwankwasiyya a Makarantar Firamare ta Dantsinke.
7. Sabunta Gina na Ajujuwan bene 8 a GSS Unguwa Uku.
8. Sabunta Gina Kwankwasiyya a GSS Unguwar Gano.
AYYUKAN TALLAFAWA HARKAKOKIN ADDINI NA ADS
1. Gina Cibiyar Ilimin Musulunci ta ADS a Masallacin Juma’a na Tarauni.
2. Gina Inuwar Tsangaya a Makarantar Malam Usaini ta Tarauni.
3. Gina Inuwar Tsangaya a Hausawa Babban Giji.
4. Gina Inuwar Tsangaya a U/Uku Kauyen Alu.
5. Gina Tsangaya a Unguwar Gano.
6. Rarraba Littatafai 5,000 da rajistar 100 ga Makarantun Islamiyya 10 a Tarauni.
7. Rarraba Dozin 10 na Tabarmi, Dozin 10 nabutoci da Janareta 5 ga Makarantun Tsangaya a Tarauni.
8. Tallafin saukar Alqur’ani ga Makarantun Musulunci 80 wanda ya kai Naira Miliyan 15.
9. Tallafin kudi ga LImamai da sauran Malamai wanda ya kai Naira Miliyan 10.
10. Gina na Ajujuwa a Makarantar Baba Umar U/uku Kauyen Alu.
AYYUKAN CI GABAN AL’UMMA DA ADS YA GUDANAR
1. Gina rijiyar burtsatse a Cibiyar Lafiya ta ADS, (PHC) Hotoro.
2. Gina rijiyar burtsatse a Unguwa Uku Kauyen Alu.
3. Gyaran Titin Hotoro Depot.
4. Gina magudanar ruwa mai nisan kilomita 0.2 a Gyadi-Gyadi Arewa.
5. Gina magudanar ruwa mai nisan kilomita 0.15* a Daurawa Layin Mai Unguwa.
6. Gyaran rijiyar burtsatse a Tarauni Layin Saleh R/Gado.
7. Gina shinge a Ofishin NSCDC dake Unguwa Uku.
8. Tallafin kudi na gyaran Transformer a Tarauni.
9. Samar da Tankin ruwa na sama a U/Uku Kauyen Alu.
SAMAR DA AYYUKAN YI DA ADS YA AIKATA
1. Samar da aikin yi na ɗindindin mai fansho ga matasa 30 a hukumomin Gwamnatin Jihar.
2. Samar da aikin wucin gadi ga matasa 10 a hukumomin Gwamnatin Jihar.
WASU KARIN AYUKAN TALLAFAWA JAM’A’A DA ADS YA YI
1. Rarraba Shinkafa ga mutane 50 a Tarauni a cikin watan Ramadan 2024.
2. Rarraba Shinkafa ga mutane sama da 300 a Tarauni a cikin Ramadan 2025.
3. Tallafin Aure ga mambobin jam’iyya da marasa galihu wanda ya kai Naira Miliyan 8.
4. Tallafin kudi ga mambobin jam’iyya da ƙungiyoyi da babbar Sallah a 2024 wanda ya kai Naira Miliyan 8.
5. Tallafin kudi ga mambobin jam’iyya da ƙungiy da babbar Sallah a 2025 wanda ya kai Naira Miliyan 15.
6. Akwai Kuma tallafin yau da kullum da al’umma suke zuwa gida ko ofis ko akan hanya da ake musu daidaiku da ma kungiyoyi

















