Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Sakamakon irin dimbin alheri da gudummawar da dan takarar majalisar tarayya na PDP, Hon. Alhaji Abubakar Ibrahim Maina, ke bai wa al’ummar karamar hukumar Tarauni, al’ummar ta sanya shi a gaba ya nemi takarar majalisar tarayya domin samun damar da zai kara hidimta musu.

Sakataren jam’iyyar PDP na mazabar Hotoro NNPC, kuma Mataimaki na Musamman ga dan takarar, Isma’ila Salihu, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya ce suna da kungiyoyi a Tarauni da ake taimakon marayu da taimakon al’umma na yau da gobe, da kuma kwamitoci da suke gudanar da tsaftace unguwanni. Akwai kuma dandamali na zauren sulhu da ake warware matsalolin da suka shafi iyaye da yara, makota, matsalar bashi da samar da masalaha, wanda dan takarar ke bayar da gagarumar gudummawa wajen gudanar da su.

Isma’ila Salihu ya ce abin da ya sa suka shiga jam’iyyar PDP, sun yi duba da abubuwa guda biyu ne. Na farko, idan aka duba irin halin da ake ciki yanzu, a zamanin PDP da ta yi mulki har ta gama, ba a taba sayen buhun shinkafa kan Naira 8,000 ba, sai dai kasa da Naira 7,000, amma yanzu ta gagari al’umma.

Ya yi nuni da cewa jam’iyyar PDP ce duk wanda ya zama wani abu a siyasa a Najeriya ya bi ta ya zama, sai dai wani abu ne ya sa ya fita ya bar ta. Don haka su ba za su bar PDP ba, domin ita ce ta yi abubuwan da ‘yan Najeriya suka mora, kuma jam’iyya ce da take yi musu sauki wajen tallatawa saboda kyawawan manufofinta, domin duk wanda ya tuna bara bai ji dadin bana ba.

Ya ce su a karamar hukumar Tarauni ba su gamsu da yadda wakilan su ke wakiltar su a jiha da tarayya ba. Mutane na kuka kan rashin kayayyakin more rayuwa, duk da akwai damarmaki da ya kamata wakilan su su kawo, ko da na ayyukan mazabu ne da ake ware musu, da za su aiwatar da su a Tarauni, wanda da su kadai Tarauni ta wuce matsayin da take a yanzu.

Isma’il Salihu ya ce idan aka duba yadda abubuwa suke gudana, idan suka bi tsarin tafiyar siyasar Ubangida, ba za su kai ga abin da suke da bukata ba na yi wa al’umma hidima, duba da yadda suke son kawo sauyi a wannan lokaci.

Don haka ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar Tarauni su zabi cancanta, wanda za su tsaya a gaban Ubangiji su fadi dalilin da ya sa suka zabe shi, domin duk abin da za ka yi, ka duba cancanta shine mafita.

“Mu muna da yakinin cewa Alhaji Abubakar Ibrahim Maina shi ne mafita, kuma muna da kyakkyawan fata a kansa saboda yadda yake taimakawa cigaban Tarauni da dukiyarsa. Idan ya zama wakilin al’ummar Tarauni a majalisa, zai kawo cigaban da ya kamata,” in ji shi.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo