Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Sha’awar ganin an sauya mummunan kallon da al’umma ke yi wa masu maganin gargajiya ce ta sanya Wazirin Magani na jihar Kano, Alhaji Nasiru Sani Abubakar, ya sadaukar da dukiyarsa wajen ɗaukar nauyin horas da masu wannan sana’a.

Wazirin Magani, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar masu maganin gargajiya ta “Moden” da kuma “QAA”, Alhaji Nasiru Sani Abubakar, ya bayyana hakan ne bayan kammala bitar kwanaki shida da aka shirya wa ƙwararru 60 masu maganin gargajiya a jihar Kano.

Bitar ta gudana ne ƙarƙashin ɗaukar nauyin kamfaninsa na Shafa’u Linnas Habal International.

Da yake jawabi, Alhaji Nasiru ya ce bitar ta yi matuƙar tasiri, domin dukkan waɗanda suka amfana da ita suna cike da farin ciki, kuma sun fahimci abubuwan da aka koya musu cikin sauƙi, duk da cewa su kansu ƙwararru ne a sana’ar.

“Wannan bita da aka yi, mutane za su yi mamaki nan gaba. Duk wani kallo da ake yi wa masu maganin gargajiya zai canza, za a ƙara samun amincewa da su sosai,” in ji shi.

Wazirin Magani, Alhaji Nasiru Sani Abubakar, ya yi kira ga ’yan uwansa masu maganin gargajiya da su ji tsoron Allah tare da tsaftace wannan sana’a mai muhimmanci da asali.

Ya ce jama’a sun ba su amana, don haka bai kamata su cutar da su ko su gallaza musu ba. Ya kuma yi kira na musamman ga masu yawo suna tallata magunguna da amsa kuwwa mai ƙarfi, musamman idan suna tare da yara ƙanana, suna shiga lungu da saƙo ba tare da kula da lokutan Sallah ko lokacin da mutane ke barci ba.

Ya ce irin wannan ɗabi’a ba ta dace da sana’ar ba, kuma ya kamata masu wannan aiki su kula da yadda suke gudanar da sana’arsu domin kare mutuncin masu maganin gargajiya a idon al’umma.

Wazirin Maganin na jihar Kano ya kuma ja hankalin waɗanda suka samu horon da kada su yi sakaci da ilimin da suka samu.

“Sun ga yadda muka wahala muka yi wannan aiki ba dare ba rana. Mun yi shi ne saboda mun san muhimmancinsa. Lallai su riƙe wannan karatu, ya zama linzami a duk inda suka zauna wajen gabatar da sana’arsu,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, shugaban Makarantar Maganin Gargajiya ta Afirka (MIJ College), Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa, ya bayyana cewa bitar ta kwanaki shida ta ba shi mamaki, tare da cewa ta tabbatar masa da cewa burin da ake da shi na ganin masu maganin gargajiya sun samu ingantaccen ilimi da ƙwarewa zai iya tabbata.

Ya yaba da yadda mahalarta bitar suka kasance masu zuwa kan lokaci tare da bin dukkan ƙa’idojin da aka gindaya.

Farfesa Jawa ya ce tun farko ba a shirya gudanar da bitar a Kano ba, sai dai kishin Wazirin Magani ya sanya aka kawo ta jihar Kano domin al’ummar jihar su amfana.

Ya ƙara da cewa: “Tun da na kafa wannan makaranta shekaru 10 da suka gabata, babu mutum ɗaya da ya taɓa ɗaukar ɗimbin kuɗi ya biya wa mutane masu wannan sana’a domin samun horo, ba ’yan uwansa ba, ba mutanen garinsu ba, saboda kawai inganta sana’a, sai Waziri. Ban ga kamarsa ba. Allah ya saka masa da alheri, ya yi matuƙar ƙoƙari,” in ji Farfesa Jawa.

Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa ya yi kira ga waɗanda suka amfana da bitar da su yi aiki da abubuwan da suka koya domin ganin manufar horaswar ta tabbata.

Ya kuma gode wa dukkan waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ganin an samu nasarar bitar, musamman waɗanda suka sadaukar da lokacinsu suka je Kaduna domin koyon ilimin, sannan suka dawo domin koyar da ’yan uwansu.

A nasa ɓangaren, Sarkin Shimfiɗa na Maganin Gargajiya na jihar Kano, Alhaji Sani Muhammad Tsamiya Babba, ya yaba da kyakkyawar niyyar Wazirin Magani wajen samar musu da wannan dama ta ƙara samun ƙwarewar zamani.

Ya kuma gode wa Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa da ya kawo musu wannan dama ta samun ƙarin ilimi da ƙwarewa tare da sanin dabarun zamani, domin inganta da bunƙasa sana’ar maganin gargajiya.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum