Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Fitaccen ɗan kasuwa a Jihar Kano kuma Shugaban Dattawan Kasuwannin Sabon Gari da Singa, Alhaji Ibrahim Ɗanyaro, ya taya al’ummar Najeriya murnar cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Alhaji Ɗanyaro ya bayyana cikar shekaru 66 da samun ’yancin kai a matsayin abin godiya ga Allah da kuma abin alfahari ga kowane ɗan Najeriya.
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya wa Najeriya albarka, Ya yaye mata dukkan matsalolin da take fama da su, Ya kuma fitar da ita daga dukkan yanayi marasa kyau.
Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su yi kyakkyawan ƙuduri na ƙaunar ƙasarsu, tare da addu’ar Allah Ya dawo da Najeriya kan hayyacinta, ta zama abin koyi ga sauran ƙasashen duniya.
Alhaji Danyaro ya jaddada cewa Najeriya ƙasa ce mai albarkatun ƙasa da mutane masu ilimi, basira da ƙwarewa. Ya ce idan talakawa da shugabanni suka haɗa kai, suka kuma yi aiki tuƙuru domin ci gaban ƙasar, da yardar Allah Najeriya za ta samu nasara tare da yin gogayya da sauran ƙasashen duniya.
A ƙarshe, Alhaji Ibrahim Danyaro ya yi addu’ar Allah Ya bai wa Najeriya alheri, Ya kuma gusar da duk wata damuwa da matsala da take fuskanta.
Ya ce akwai ƙasashe da dama a duniya da suka taɓa shiga irin wannan yanayi na matsaloli, amma daga baya suka samu nasarar shawo kansu. Don haka, ya roƙi Allah Ya bai wa Najeriya haɗin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali.






