Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugaban Majalisar Ƙungiyoyi Masu Sanya Kayan Sarki (Council of Uniform Voluntary Organizations), reshen Jihar Kano, Magaji Ibrahim Tudun Wada, ya buƙaci Gwamnatin Jihar Kano da ta ƙara tallafa wa majalisar domin inganta ayyukan da take gudanarwa a faɗin jihar.
Magaji Ibrahim Tudun Wada, wanda kuma shi ne Kwamishinan Scout na Jihar Kano, ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan yadda majalisar ta bayar da gudunmawa a bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Filin Wasan Ƙwallon Ƙafa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.
Ya ce majalisar tana gudanar da ayyukanta ne da ƙoƙarin kanta, sai dai a wasu lokuta tana rubuta takarda ta nemi tallafi daga Gwamnatin Jihar Kano, wadda yake cewa tana ba su tallafi.
Ya bayyana cewa daga cikin ayyukan majalisar akwai ƙoƙarin dakile amfani da kayan sarki irin na hukumomin gwamnati ba tare da izini ba, da kuma hana ɗaukar sanduna ko wasu abubuwa masu kama da makamai yayin bukukuwan hawan sarki.
Ya ce majalisar ta kuma hana duk wata ƙungiya da ba ta cikin cikinta amfani da kayan sarki ba tare da izini ba, domin tabbatar da bin doka da kuma kare al’adu da tarbiyyar al’ummar Kano.
Magaji Ibrahim ya ce kowace ƙungiya tana da nata dokoki, amma yanzu duk ƙungiyoyin sun haɗa kansu a ƙarƙashin Majalisar Ƙungiyoyi Masu Sanya Kayan Sarki ta Jihar Kano, wadda ke kula da ayyukan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta.
Ya ce duk lokacin da wata ƙungiya ta yi wani abu da bai dace da tarbiyya da al’adar Jihar Kano ba, majalisar tana ɗaukar matakan da suka dace domin dakile hakan.
Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta fahimci muhimmiyar gudunmawar da majalisar ke bayarwa wajen hana faɗa da faɗace-faɗacen daba, da kuma sauran abubuwan da ka iya kawo rashin tarbiyya da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Magaji Ibrahim Tudun Wada ya ce akwai ƙungiyoyi sama da 1,000 a Jihar Kano, amma bayan tantancewa da rajista, ƙungiyoyi 25 ne suka samu cikakken rijista a ƙarƙashin majalisar, inda aka tabbatar da wuraren da kowace ƙungiya take gudanar da ayyukanta.
Ya ce a halin yanzu suna fuskantar wasu ƙalubale, ciki har da rashin ofishin gudanar da ayyuka da kuma motar da za ta taimaka wajen gudanar da ayyukansu a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa majalisar tana da rassa a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, don haka samun ƙarin tallafi daga gwamnati zai taimaka wajen inganta da bunƙasa ayyukanta.
A nasa ɓangaren, Sakataren Majalisar Ƙungiyoyi Masu Sanya Kayan Sarki ta Jihar Kano (Council of Uniform Voluntary Organization, Kano), Ibrahim Khalil Fagge, wanda ke aiki da Rundunar Yaƙi da Rashin Da’a ta Jihar Kano, ya ce majalisar ta samu nasarori da dama, musamman wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa.
Ya ce suna ƙoƙarin magance matsalar tun daga tushe ta hanyar wayar da kan matasa game da illolin shaye-shaye, da kuma koyar da su muhimmancin neman ilimi, dogaro da kai da kuma kasancewa masu ɗa’a da biyayya a cikin al’umma.
Ibrahim Khalil Fagge ya ce suna kallon nasarar gyaran tarbiyya a tsakanin matasa a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da majalisar ke alfahari da su.
Ya ƙara da cewa suna shirin ɗaukar wasu matakai tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin masu Adaidaita Sahu da masu amfani da TikTok, domin dakile yaɗuwar hotuna da bidiyoyin da ba su dace ba a jikin baburan Adaidaita Sahu da kuma shafukan TikTok, musamman waɗanda ke ɗauke da abubuwan da suka shafi shan miyagun ƙwayoyi.






