Daga Ibrahim Muhammad, Kano
A daidai lokacin da Najeriya ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, wani matashi a Jihar Kano, Abdulkarim Balarabe Shehu daga Unguwar Zango, ya yi kira ga shugabanni a matakai daban-daban da Allah Ya ɗora wa alhakin ci gaban al’umma da su ƙara tallafa wa matasa, waɗanda ya bayyana a matsayin kashin bayan ci gaban al’umma.
Ya ce matsaloli da dama da ke faruwa a cikin al’umma suna da alaƙa da matasa, musamman idan suka tashi ba tare da sana’a ko abin dogaro ba. Saboda haka, ya buƙaci gwamnati da ta ƙara ƙoƙarin tallafa wa matasa tare da samar musu da sana’o’in dogaro da kai.
Abdulkarim ya ce gwamnati ya kamata ta ƙara ƙoƙari wajen koyar da matasa sana’o’i, domin matasa suna taka muhimmiyar rawa a harkokin gwamnati da al’umma.
Ya ce a duk lokacin da za a gudanar da wani babban taro ko wani muhimmin aiki, matasa ne ake yawan sanya a gaba, musamman ’ya’yan talakawa. Haka kuma, a lokacin zaɓe ana amfani da matasa wajen gudanar da ayyuka daban-daban har zuwa lokacin da ake samun nasarar zaɓe.
Ya ce duk da cewa Gwamnatin Jihar Kano tana ƙoƙari wajen tallafa wa matasa, akwai matsalar rashin isa ga waɗanda tallafin ya kamata ya ratsa, saboda wasu daga cikin waɗanda ake ba tallafin ba sa isar da shi ga matasan da aka yi niyyar tallafa wa.
Ya yi kira ga gwamnati da ta riƙa bibiyar duk wani tallafi da ta bayar domin matasa, don tabbatar da cewa ya isa ga waɗanda aka yi niyyar tallafa wa.
Ya kuma buƙaci gwamnati da ta riƙa bai wa shugabannin ƙananan hukumomi isasshen tallafi domin su tallafa wa matasa, kasancewar su ne suka fi kusa da al’umma kuma suka fi sanin matasan da ke buƙatar tallafi a yankunansu.
Abdulkarim ya ƙara da cewa ya kamata Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara ɗaukar matakan sa ido da bibiya domin tabbatar da cewa duk wani tallafin da ta bai wa matasa ya isa gare su.
Ya kuma shawarci matasan da suka amfana da tallafin da su yi amfani da abin da suka samu yadda ya kamata, domin su amfana da shi tare da samar da ci gaba ga kansu da al’umma.
A ƙarshe, Abdulkarim Balarabe Shehu Zango ya yi kira ga al’ummar Najeriya da su ci gaba da yi wa ƙasar addu’ar samun zaman lafiya, tare da roƙon Allah Ya sa zaɓukan da ke tafe su gudana cikin lumana, Ya kuma zaɓa wa ƙasar shugabanni na gari.






