
Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar mata, Maryam Suleiman, saboda sukar da ta yi wa Gwamna Uba Sani kan makudan bashin da ya gada daga gwamnatin da ta gabata.
Kamar yadda mai magana da yawun gwamna Sani, Alhaji Mohammed Shehu, ya shaida wa jaridar PUNCH, gwamnan ya yi watsi da sukar da dan gwamnan da ya shude, Nasir El-Rufai, Bashir, ya yi masa.
Jam’iyyar APC ta Kaduna, a sanarwar da ta fitar a ranar 31 ga Maris, 2024, ta ce an dakatar da shugabar matan ne bisa sukar da ta yi wa gwamna Uba Sani a kafafen watsa labarai.
Shugaban jam’iyyar APC na yankin Badarawa/Malali Ali Maishago da Zakkah Bassahuwa ne suka sanya hannu kan sanarwar dakatarwar.
Jam’iyyar ta zargi Maryam Suleiman da aka fi sani da Maryam Mai Rusau da aikata ayyukan bata sunan gwamnan.
Gwamnan jihar Kaduna, a ranar Asabar din da ta gabata, a yayin wani taron ganawa da yake yi da al’umma da ake kira Town Hall Meeting da Turanci, ya koka da dimbin bashin da ya gada daga magabacinsa, El-Rufai.
Sani ya ce an bar jihar da ‘yan kudin da ba su taka kara suka karya ba, wanda bai isar su biyan albashin ma’aikata.
Gwamnan ya ce El-Rufai ya bar masa bashin Dala miliyan 587 da N85bn da kuma bashin kwangila 115.
“Duk da dimbin basussukan da suka kai $587m, N85bn, da kuma bashin kwangilar N115bn da muka gada daga gwamnatin da ta shude, mun tsaya tsayin daka wajen ganin jihar Kaduna ta samu ci gaba mai dorewa.”
Sani ya ce; “Mun gudanar da cikakken nazari kan halin da muke ciki, kuma muna kara mayar da hankali kan hakan.”
Sai dai shugabar matan ta jam’iyyar APC da ke magana da harshen Hausa a wata hira aka yi da ita a kafar yada labarai ta DCL Hausa, ta caccaki gwamnan kan kalaman nasa, inda ta bayyana shi a matsayin mai butulci.

A cikin wannan hirar ta zargi Gwamna Uba Sani da rashin iya gudanar da mulki, tare da shawarce shi da ya guji alakanta gazawarsa ga El-Rufai.
Ta kuma shawarce shi da in ba zai iya mulkin ba ya sauka ya ba wanda zai iya wuri.
Sai dai a sanarwar dakatarwar, jam’iyyar APC ta Kaduna ta yi zargin cewa Maryam Suleiman na da hannu wajen kitsa harin da aka kai wa mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa, Manzo Maigari, da wasu ‘yan daba suka kai.
A halin da ake ciki, mai magana da yawun gwamna Sani ya shaida wa jaridar PUNCH cewa gwamnan ba zai mayar da martani ga dan El-Rufai ba, wanda ya soki gwamnan kan bayanin da ya yi a kan bashin da ake bin jihar.
Dan El-Rufai, Bashir, a shafinsa na sada zumunta, ya zargi magajin mahaifinsa Sani, da yin watsi da nauyin da ya rataya a wuyansa ta hanyar kaurace wa jihar kodayaushe yana galafiri a Abuja.
Bashir El-Rufai ya zargi gwamnan da kewaye kansa da wasu mukarraban da aka nada domin goyon bayan siyasa ba don kawo ci gaban jihar Kaduna ba.
Sai dai da aka nemi ya mayar da martani kan ikirarin Bashir, mai magana da yawun gwamnan ya ci gaba da cewa shugaban nasa ya bayyana karara kan halin kudin jihar.
“Aikin da ke gabanmu yana da girma, kuma ba za mu bata lokacinmu wajen cece-kuce ba hakan da abubuwan da ba su da amfani ba. Mai girma Sanata Uba Sani ya riga da ya bayyana hakikanin halin da jihar ke ciki,” in ji Shehu.






