Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ma’ajin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Gezawa, Hon. Sani Muhammad Jogana, ya ce kyakkyawan wakilcin ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar Gezawa, Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara, ya sa jam’iyyar APC ta yi nisa a siyasa, har jam’iyyun adawa suka rasa tasiri a yankin.
Hon. Jogana, wanda kuma shi ne mataimaki na musamman ga Hon. Tsamiyar Kara kan ayyuka, ya bayyana cewa ’yan takarar jam’iyyun adawa ba su da ƙwarin gwiwar da za su iya kayar da APC, yana mai cewa babu wanda ya cancanci samun goyon bayan al’umma a cikinsu.
Ya ce har yanzu ba a san waɗanda za su tsaya takarar jam’iyyun NDC da ADC a Gezawa a zaɓe mai zuwa ba, yana mai cewa jam’iyyun sun kasa haɗa kansu, yayin da APC ke jiran ranar zaɓe kawai.
“Jam’iyyar APC ita ce jam’iyyar talakawa. Idan aka duba jagoranmu, Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara, tun bayan ƙirƙirar ƙaramar hukumar Gezawa, ba a taɓa samun wakilci irin nasa ba. Duk abin da ya samu na haƙƙin al’umma, yana kai wa al’ummar kai tsaye,” in ji Hon. Jogana.
Ya ƙara da cewa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Gezawa da Gabasawa, Hon. Nasir Laraba, shi ma yana gudanar da kyakkyawan wakilci. Haka kuma, ya bayyana ɗan takarar sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, a matsayin mutum mai gaskiya da riƙon amana.
Dangane da gwamnatin jihar Kano, Hon. Jogana ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gudanar da ayyukan raya ƙasa da suka jawo sha’awar al’ummar wasu jihohi, waɗanda yake ganin suna fatan samun irin wannan jagoranci saboda ayyukan da gwamnan ya shimfiɗa a sassa daban-daban na jihar.
Game da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Hon. Jogana ya ce shugaban yana ƙoƙarin ciyar da ƙasar gaba. Ya bayyana cewa addu’arsu ita ce Allah Ya ba shi damar ci gaba da mulki bayan zaɓen 2027, domin ya kammala ayyukan da ya fara.






