PDP Za Ta Kawo Ƙarshen Rashin Aikin Yi a Tsakanin Matasa a Nasarawa, Kano -Jamilu

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ɗan takarar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa Kano a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Hon. Jamilu Muhammad Ahmad, ya bayyana bikin al’adar Yawal da al’ummar Marghi mazauna jihar Kano suka gudanar a matsayin abin farin ciki da kuma babbar nasara ga al’ummar.

Hon. Jamilu ya bayyana hakan ne bayan halartar bikin al’adar Yawal da kuma bikin cika shekara guda da naɗa Sarkin Marghi na Kano, Ptil Marghi Wadzani Adamu Mamza, a kan karagar mulki.

Ya ce abin a yaba ne yadda al’ummar Marghi suke riƙe da al’adunsu tare da ƙoƙarin tabbatar da dorewarsu. Ya ƙara da cewa, idan aka yi la’akari da yawan ƙabilun da ke zaune a jihar Kano, ƙaramar hukumar Nasarawa na daga cikin wuraren da ke da al’ummomi masu bambancin ƙabila da al’adu.

A cewarsa, ƙaramar hukumar Nasarawa tana da kusan kashi 75 cikin 100 na ƙabilu daban-daban da ke zaune a kananan hukumomin jihar, inda ake ba kowa haƙƙinsa da darajarsa a matsayin ɗan ƙasa.

Ya ce, “Nasarawa tamkar ƙaramar Najeriya ce. Duk lokacin da mutum ya zo neman mulki, dole ne ya ba kowa haƙƙinsa na ɗan ƙasa.”

Da yake tsokaci kan matsalolin da yankin ke fuskanta, Hon. Jamilu ya bayyana rashin aikin yi a tsakanin matasa a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar ƙaramar hukumar Nasarawa a halin yanzu.

Ya ce a matsayinsa na matashi kuma ɗan takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, sun fahimci girman matsalar rashin aikin yi, musamman ganin cewa yankin na da wuraren da za a iya samar da ayyukan yi ga matasa, amma rashin mayar da hankali daga wasu ’yan siyasa ya hana cimma wannan buri.

Hon. Jamilu ya ƙara da cewa, idan Allah Ya ba su damar samun nasara, za su yi ƙoƙarin samar da hanyoyin magance rashin aikin yi da kuma kawo ƙarshen zaman banza a tsakanin matasa.

Ya ce za su yi amfani da damar da yankin ke da ita wajen samar da ayyukan yi, tare da tabbatar da cewa an yi la’akari da tsarin zamantakewar al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa, wadda ta ƙunshi ƙabilu da al’adu daban-daban.

Saboda haka, ya yi kira ga al’ummar Nasarawa da su ci gaba da zaman lafiya da juna, tare da riƙe kyakkyawar alaƙar da aka san yankin da ita, ba tare da nuna bambancin ƙabila ko addini ba.

Haka kuma, Hon. Jamilu Muhammad Ahmad ya yaba wa al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa bisa goyon baya da haɗin kan da suke bai wa takararsa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP. Ya buƙace su da su ci gaba da mara wa jam’iyyar baya tare da zaɓenta a zaɓe mai zuwa.

Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu, ƙaramar hukumar Nasarawa na daga cikin wuraren da jam’iyyar PDP ke da ƙarfi da tasiri a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin shugaban matasan jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ibrahim Bala Aboki, da shugaban PDP na jihar Kano, Alhaji Rabiu Wangal.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength