Al’ummar Nasarawa Sun Karrama Farfesa Tsauni Bisa Naɗinsa a Matsayin Mataimakin Shugaban BUK

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano sun gudanar da bikin karrama Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni bisa naɗa shi a matsayin mataimakin shugaban jami’ar Bayero ta Kano (DVC) mai kula da harkokin ilimi.

An gudanar da bikin ne a ranar Asabar a ɗakin taro na ɗakin karatu na Murtala Muhammad da ke Kano, inda manyan baƙi daga sassa daban-daban suka halarta, ciki har da farfesoshi, masu sarauta, malamai, ɗalibai da sauran al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana wanda aka karrama a matsayin mutum mai jajircewa, hazaka da ƙwazo, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban jami’ar a fannoni daban-daban.

Ya ce Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni ya taɓa riƙe shugabancin sashen tattalin arziki, sannan ya yi aiki a matsayin darakta a sashen wallafa mujallu na Jami’ar. Ya ƙara da cewa farfesan ya daɗe yana bayar da gudunmawa a fannonin koyarwa, bincike da gudanar da ayyuka a Jami’ar Bayero.

Farfesa Haruna Musa ya bayyana cewa gudunmawar da Farfesa Tsauni ya bayar tana da yawa, yana mai cewa sanin halayensa ya sa ya tabbatar da cewa mutanen unguwar Tsauni ma ba za su iya saninsa fiye da yadda ya san shi ba. Ya ce duk da kasancewarsa babbansa, Farfesa Tsauni ya shafe sama da shekaru 10 yana koyarwa kafin shi ma ya fara aiki. Sai dai tun daga lokacin da ya fara aiki zuwa yanzu, sun ci gaba da kasancewa cikin kyakkyawar alaƙa. Ya ƙara da cewa Farfesa Tsauni ya jagoranci fafutukar da aka yi har aka zaɓe shi a matsayin shugaban Jami’ar Bayero.

Shi ma wanda aka karrama, Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni, ya bayyana farin cikinsa bisa irin ƙauna da zumuncin da al’ummar Tsauni, Badawa, Giginyu, Kawo da ƙaramar hukumar Nasarawa baki ɗaya suka nuna masa ta hanyar shirya masa irin wannan karramawa, wadda ya ce ita ce ta farko a tarihinsa.

Ya ce ya yi matuƙar farin ciki da wannan karamci, har ya kasa samun kalmomin da za su bayyana godiyarsa ga kowa, sai dai ya roƙi Allah Ya saka wa kowa da alheri.

Farfesa Tsauni ya yi alƙawarin ci gaba da yi wa al’umma hidima ta hanyar riƙe amana, gaskiya da kiyaye mutuncinsa, domin tabbatar da cewa bai ba su kunya ba.

Ya kuma alƙawarta ƙara ƙaimi da jajircewa wajen sauke dukkan amanar da ke kansa a jami’ar Bayero cikin gaskiya da riƙon amana, tare da yin duk abin da zai ƙara wa jami’ar daraja da guje wa duk wani abu da zai iya kawo mata koma-baya.

Ya gode wa dukkan waɗanda suka halarci taron, tare da yi musu addu’ar Allah Ya faranta musu rai, Ya albarkace su, sannan Ya fito da wasu mutanen kirki daga cikinsu waɗanda za su zarce shi wajen hidima ga al’umma.

Da yake zantawa da manema labarai, shugaban kwamitin shirya taron, Alhaji Kabiru Idris Abdullahi Tsauni, ya ce labarin naɗin ɗan uwansu a wannan babban matsayi ne ya sa suka haɗa kai suka kafa kwamiti domin shirya bikin karramawar.

Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan da suka sa suka yanke shawarar karrama Farfesa Tsauni shi ne yadda yake nuna ƙauna da kulawa ga al’ummar garinsu a duk lokacin da ya je gida.

A cewarsa, Farfesan yana mu’amala da kowa cikin mutunci, daga yara har zuwa manya, tare da karɓar su hannu bibbiyu da kuma ba matasa shawarwari masu amfani.

Ya ƙara da cewa Farfesa Tsauni yana ƙarfafa wa yara gwiwa wajen neman ilimi, kuma ya taimaka wa da dama daga cikinsu. Har ma yana bin diddigin yaran da suka daina zuwa makaranta, yana ba su shawara tare da ƙarfafa musu gwiwa su koma karatu, su gyara takardunsu, sannan su ci gaba da karatu a manyan makarantu.

Alhaji Kabiru Idris Abdullahi ya ce ladabi, biyayya, aiki tuƙuru da jajircewa su ne manyan abubuwan da suka taimaka wa Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni wajen samun ɗaukaka a Jami’a.

Ya ce a duk lokacin da aka ba shi wani aiki na musamman, yana gudanar da shi cikin gaskiya da riƙon amana, abin da ya ce ya taimaka wajen ƙara masa daraja a idon shugaban jami’ar saboda yadda yake gudanar da ayyukansa domin ci gaban Jami’ar Bayero.

A yayin taron, ƙungiyoyi daban-daban sun miƙa takardun shaidar karramawa ga Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni. Shi ma farfesan ya bai wa Malam Abdulkadir Husain Kanya, wanda ya koyar da shi a makarantar firamare, kyauta ta musamman domin nuna godiya da girmamawa gare shi.

Haka kuma, Malam Kabiru Bala ya gabatar da taƙaitaccen tarihin rayuwar Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni, tun daga haihuwarsa da makarantun da ya yi zuwa matakan da ya bi har ya kai ga wannan babban matsayi.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Babban Khadi na jihar Kano, Tijjani Yusuf Yakasai; Farfesa Binta Tijjani Jibrin, masaniyar tattalin arziƙi a Jami’ar Bayero kuma tsohuwar kwamishiniya a jihar Kano; da shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Yusuf Imam Ogan Boye, wanda Hon. Bala Khalid ya wakilta a wajen taron, da sauran manyan baƙi.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength