Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya mai kula da Shiyya ta Ɗaya (Zone One) mai hedikwata a Kano, AIG Garba Ahmed, ya kai ziyarar duba sabon ofishin rundunar Special Protection Unit (SPU), Base 1, da aka gina a Tabarakallah Layout, kan hanyar Gwarzo a Kano.
AIG Garba Ahmed ya gudanar da ziyarar ne tare da tawagar gudanarwa ta hedikwatar Zone One, domin duba matakin kammala ginin ofishin.
An bayyana cewa samar da sabon ofishin na daga cikin ƙoƙarin Rundunar ‘Yan Sanda na faɗaɗa ayyukanta, domin ƙara inganta tsaro a Shiyyar da ta ƙunshi jihohin Kano da Jigawa.






