Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Kwararren dan jarida a Jihar Kano da ma Najeriya baki daya, Dakta Garba Ubale Dambatta, ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa matakin da ya dauka na cire tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, daga mukaminsa.
A cikin wata sanarwa da Dakta Garba Ubale Dambatta ya aikawa ‘yan jarida, ya bayyana cewa ayyukan da tsohon Kwamishinan ya gudanar sun fi kama da na kungiyoyin gwagwarmaya fiye da na aikin jarida na gaskiya da zai daga darajar fannin a fadin Jihar Kano.
“A matsayinmu na wadanda suka shafe fiye da shekaru 30 muna aikin jarida, muna yaba wa Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, da matakin da ya dauka na cire tsohon Kwamishinan Yada Labarai daga kujerarsa, saboda kusan ba aikin jarida ya yi ba, aikin da ya yi irin na ‘yan gwagwarmaya ne, wanda hakan kusan a iya cewa koma baya ne, domin ya ci karo da sharudda da ka’idojin aikin jarida,” in ji Dakta Dambatta.
“Irin abubuwan da ya rika jawowa Jihar Kano sun jawo mata mummunar fahimta daga kungiyoyin da ke sa ido kan harkar aikin jarida da kuma hakkin ‘yan jarida, abin babu dadin ji,” in ji shi.
Dakta Garba Ubale Dambatta ya yi fatan a wannan karon Mai Girma Gwamna zai ajiye kwarya a gurbin ta, ta hanyar nada wanda ya cancanta kuma yake da kwarewa a fannin aikin jarida da kuma kyakykyawar mu’amala da ‘yan jarida, domin kawo gyara a aikin da kuma dawo da martabar aikin jarida a Jihar Kano.
“Matukar Gwamnan Kano ya yi mana haka, mu kuma a shirye muke mu ci gaba da bada dukkan wata gudummawa da shawarwari da za ta taimaka wajen kyautata aikin tare da daga darajar sa a Jihar Kano a idon duniya,” in ji Dambatta.
Garba Ubale Dambatta dai ya shafe sama da shekaru 30 yana aikin jarida a ciki da wajen Najeriya. Ya taba aiki da Sashen Hausa na DW Hausa da ke birnin Bonn a kasar Jamus, Sashen Hausa na Daily Trust, Mataimakin Edita na Jaridar Rariya, Edita na Hamada Radio da ke Abuja, Shugaban Sashen Hausa na gidan Radiyon Kiss FM da ke Abuja, kafin ya koma Radio Nigeria a matsayin Manaja.
Dama dai ana ta kokawa akan yanda Waiya yake gudanar da harkar ma’aikatar yada Labarai da rashin kwarewa da hakan ke jawowa harkokin ingiza manufofin Gwamnatin koma baya






