Sabuwar Dokar NCC Za Ta Jefa ’Yan Kasuwar Waya Cikin Mawuyacin Hali –Jamilu Bala Gama

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Zababben shugaban ƙungiyar masu sana’ar saye da sayar da wayoyi da kayayyakin haɗi ta ƙasa (AMPAT) reshen jihar Kano, kuma zaɓaɓɓen shugaban kasuwar wayoyi ta Farm Centre, Ambasada Jamilu Bala Gama, ya bayyana damuwarsa kan sabuwar dokar da Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta bullo da ita, yana mai cewa dokar na iya jefa ’yan kasuwar wayoyi cikin mawuyacin hali tare da kawo cikas ga harkokin kasuwancinsu.

Ambasada Jamilu Bala Gama ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya ce a matsayinsu na ’yan ƙasa kuma masu ruwa da tsaki a harkar wayoyi, suna ganin lokacin da hukumar ta zaɓa na aiwatar da sabuwar dokar bai dace ba.

Ya ce ya kamata duk wata sabuwar manufa da gwamnati ko wata hukuma za ta ɓullo da ita, musamman wadda ta shafi harkokin kasuwanci, a sanar da al’umma tun da wuri, domin su fahimci manufar tare da samun isasshen lokaci na shirin tunkarar sauye-sauyen ba tare da an cutar da sana’arsu ko al’ummar da suke hulɗa da su ba.

Jamilu Bala Gama ya yi kira ga mahukunta da su dakatar da aiwatar da dokar tare da sake duba wa’adin da aka ba ’yan kasuwar wayoyin, domin tabbatar da cewa matakin ba zai jefa masu sana’ar cikin asara ko kuma ya ƙara wa masu sayen wayoyi wahala ba.

Ya bayyana cewa lokacin da NCC ta sanar da sabuwar dokar, ta ba su ɗan gajeren lokaci, wanda bai wuce makonni biyu zuwa wata guda ba. Ya ƙara da cewa hukumar ta gayyace su ne kawai zuwa ofishinta da ke Kano, inda ta yi musu taƙaitaccen bayani kan dokar tare da sanar da su cewa za ta fara aiki nan ba da jimawa ba.

Shugaban ya ce sun riga sun aika da wasiƙu daban-daban zuwa ga hukumar NCC domin bayyana damuwarsu da illolin da suke ganin dokar za ta iya haifarwa ga masu sana’ar wayoyi da sauran al’umma, musamman masu ƙaramin ƙarfi.

Ya ce dokar ta zo musu ne ba-zato-ba-tsammani, don haka suke ganin ya kamata a sake duba yadda za a aiwatar da ita domin kauce wa ƙarin matsin tattalin arziƙi ga ’yan kasuwa da masu sayen wayoyi a Najeriya.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo