Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Al’ummar ƙaramar hukumar Birnin Kano, ciki har da ’yan siyasa, ’yan uwa da abokan arziƙi, sun raka jagoran jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar, Hon. Muktar Ishaq Yakasai, zuwa Ma’aikatar Jinƙai ta Jihar Kano, a safiyar Litinin, domin fara aiki a matsayin sabon kwamishinan ma’aikatar.
Da yake jawabi ga ma’aikatan ma’aikatar da kuma al’ummar da suka raka shi, Hon. Muktar Ishaq Yakasai ya gode musu bisa ƙauna da amincewar da suka nuna masa, yana mai cewa zai yi amfani da damar da Allah ya ba shi wajen kyautata rayuwar al’umma.
Ya bayyana cewa babu wani ɗan Adam da zai iya gamsar da kowa, domin Allah ne kaɗai ke da ikon hakan. Ya ce za su yi iya ƙoƙarinsu wajen gudanar da ayyukan da suka dace, amma rabon kowa yana hannun Allah.
“Abin da Allah ya ba mu iko za mu yi. Wanda Allah ya ƙaddara zai samu wani abu a cikin harkar, zai samu, wanda kuma Allah bai nufa da rabonsa ba, ko da kana da kusanci da mai rabon, ba za ka samu ba,” in ji shi.
Kwamishinan ya ƙara da cewa ya kamata al’umma su fahimci cewa ba gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ko shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ko shugaban ƙaramar hukuma, ko kwamishina ne zai iya gamsar da kowa ba. Sai dai ya tabbatar da cewa da kyakkyawar niyya da tsari, za su yi iya ƙoƙarinsu wajen sauke nauyin da ke kansu.
Ya bayyana cewa Ma’aikatar Jinƙai ofishin al’umma ce, wadda aka kafa domin taimakawa da tallafa wa masu buƙata, yana mai cewa sun zo ne da niyyar yin aiki domin amfanin jama’a. Ya kuma roƙi al’umma da su ci gaba da yi musu addu’a, tare da gode wa duk waɗanda suka samu damar raka shi.
Da yake jawabi ga ma’aikatan Ma’aikatar, Hon. Yakasai ya ba su tabbacin cewa za su yi aiki tare cikin haɗin kai domin bunƙasa Ma’aikatar da gudanar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen ci gaban al’umma.
A nasa jawabin, Babban Sakataren Ma’aikatar Jinƙai ta Jihar Kano, Alhaji Babani, ya bayyana sabon kwamishinan a matsayin mutum mai jajircewa da ƙwazo wajen gudanar da ayyuka.
Ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatan Ma’aikatar za su ba shi cikakken haɗin kai da goyon baya domin samun nasarar ayyukansu.
Shi ma Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, Hon. Salim Hashim, ya bayyana farin cikinsa da zuwan sabon kwamishinan, yana mai cewa ya yi sa’a da ya samu kansa a cikin ma’aikata masu kishin ci gaban jihar Kano.
Ya ce ma’aikatan Ma’aikatar ma sun yi dace da samun kwamishina nagari, wanda ya bayyana a matsayin mutum mai adalci, tausayi da rashin hassada. Ya kuma nuna fatan cewa haɗin kansu zai taimaka wajen kawo ci gaba ga jihar Kano.
A nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Kano, kuma Shugaban Ƙungiyar Shugabannin APC na Jihar Kano, Ambasada Munzali Danbazau, ya taya sabon kwamishinan murna tare da yi masa fatan alheri a sabon muƙamin da ya samu.
Ya ce Hon. Muktar Ishaq Yakasai mutum ne da aka sani da ƙoƙarin tabbatar da haɗin kan al’ummar ƙaramar hukumar Birnin Kano. Ya ƙara da cewa shugabannin APC na ƙaramar hukumar za su ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa jam’iyyar da tallafa wa manufofin da za su inganta rayuwar al’umma, domin tabbatar da an samu ribar dimokuraɗiyya.






