Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Al’ummar karamar hukumar Makoda sun bayyana cikakken yakinin cewa za su samu ingantacciyar wakilci daga dan takarar su na majalisar dokokin Jihar Kano a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya, Hon. Dakta Saleh Musa Wailare.
Al’ummar sun bayyana hakan ne bisa la’akari da irin gudummawar da yake bayarwa ba ga al’ummar Makoda kadai ba, har ma da ta karamar hukumar Dambatta, wajen tallafawa cigaban su a fannoni da dama ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.
Da yawa daga cikin al’ummar sun ce Dakta Saleh Musa Wailare, ta karkashin gidauniyarsa ta Malam, ya dade yana tallafawa al’umma ba don siyasa ba, kasancewar shi mutum ne mai tausayi da jinkai wanda burinsa shi ne ganin ya daga darajar al’umma musamman matasa maza da mata, tare da taimakawa harkar ilimi tun daga tushe.
Sun ce matasa da yawa wadanda ba za a iya lissafa adadinsu ba, Dakta Saleh Musa Wailare ya samar musu da aikin yi a hukumomin Gwamnatin Tarayya daban-daban, musamman a bangarorin jami’an tsaro da suka hada da Soja, ‘Yan Sanda, Civil Defence, Immigration, Customs da dai sauransu.
Sun jaddada cewa duk wannan hidima da yake yi, ba don neman wani matsayi na siyasa yake yi ba, sai don jinkai da son taimakawa al’umma. Don haka suka ce duk wanda ke hidimar al’umma da dukiyarsa ba tare da yana da mukami ba, suna da yakinin idan ya samu dama zai ninka abin da yake yi a baya.
Wani jigo a jam’iyyar APC a Makoda da ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaron siyasa ya ce, magana ta gaskiya takarar da Dakta Saleh Musa Wailare ke yi ta majalisar dokokin Jihar Kano a jam’iyyar NDC, takara ce ta al’umma baki daya.
A cewarsa, shi ne dan takara daya tilo da kowa zai iya zabarsa ba tare da la’akari da jam’iyya ba, domin ayyukansa na alkhairi a bayyane suke.
Ya ce Hon Dakta Saleh Musa Wailare shi ne mutumin da ke da gidauniya mai taimakawa mata, matasa, iyaye, malamai da makarantu, duk wani aiki na jinkai yana gudanarwa ga al’ummar Makoda har ma da Dambatta, don haka ya cancanci ya zama wakili na al’umma.






