Gwamnan Zamfara Ya Cira Wa Jami’an Tsaro Hula, Ya Jajanta Wa Jama’a

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya jinjna wa ƙoƙarin jami’an tsaro na haɗin gwiwa game da sabbin hare-hare da nasarorin da su ke samu a kan ‘yan bindiga a jihar.

A ƙarshen makon da ya gabata, rundunar sojojin ƙasar nan ta aika da wasu ƙarin jami’an ta, a wani yunƙuri na sake fatattakar ayyukan ‘yan bindiga a yankunan da abin ya yi ƙamari a jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau yau, ya bayyana dirar mikiyar da sojojin suka yi wa ‘yan bindigar a matsayin mataki na dagula harkokin miyagun ‘yan ta’addan a Zamfara.

Sanarwar ta Sulaiman Bala ta kuma jajanta wa al’ummomin da harin ‘yan bindigar ya shafa a ‘yan kwanakin nan, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar na nan tana ci gaba da baiwa jami’an tsaro cikakken haɗin kai don shawo kan lamarin.

Sanarwar ta ce: “Ayyukan yaƙin da sojoji ke gudanarwa a wuraren da rashin tsaro ya yi ƙamari a Zamfara, abin a yaba ne, musamman bisa la’akari da irin nasarorin da aka samu tun lokacin fara ƙaddamar da munanan hare-hare kan ‘yan ta’addan a ƙarshen makon da ya gabata.

“Wannan aiki ya samu Gagarumar nasara a yankunan Ƙananan Hukumomin Bungudu, Tsafe, Maru, da Zurmi, wanda ta kai ma hallaka wani ƙasurgumin ɗan ta’adda, Abu Dan Dunkwuifa, wanda ya yi fice wajen addabar wasu ƙauyuka a Bungudu da Maru.

“A ƙauyen Magama Mai Rake ta yankin Dansadau da ke Ƙaramar Hukumar Maru, jami’an tsaron sun samu nasarar hallaka gomomin ‘yan ta’adda.

“Harin da sojoji suka sake kai wa a Nasarawan Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum ya yi sanadiyyar ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su a ƙauyukan Kamaru, Tungar Rogo, da Matsare, tare da ƙwato shanu da dama da aka sace.

“Jita-jitar cewa an yi garkuwa da mutane sama da 500 ƙarya ce ta wasu mutane da ba sa son zaman lafiya ya dawo Jihar Zamfara. Mafi akasarin yankunan da ke fama da rashin zaman lafiya a Zamfara na ci gaba da samun taimakon soji, inda ake samun sakamako mai kyau.

Gwamnan ya kuma jajanta wa al’ummar da ’yan bindiga suka kai wa hari a jihar.

“Gwamnatin jihar Zamfara na son nuna alhini ga al’ummomin da ’yan bindiga suka kai wa hari kwanan nan. Mun himmatu sosai wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Gwamnatin mu za ta ci gaba da tallafawa sojojin da ke yaƙi da rashin tsaro tare da bayar da duk wani tallafin gaggawa ga waɗanda rikicin ‘yan bindiga ya shafa a jihar.”

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History