
Daga Abubakar Rabilu Gombe
Kimanin Manyan Mata da Yan Mata 50 ne suka ci gajiyar aikin tiyatar yoyon fitsari 1kyauta da UNFPA ta dauki nauyin yi a Gombe.
Hukumar UNFPA ta gudanar da jinyar kyauta ne tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Gombe tare da tallafin gidauniyar Fistula da gwamnatin kasar Norway.
An gudanar da aikin tiyatar ne a asibitin kwararru na jihar Gombe kuma babban daraktan kula da lafiya na asibitin Dakta Mu’azu Shu’aibu ya ce an yi hakan ne saboda nuna juyayi kan halin da matan ke ciki a duk lokacin da suka samu kansu da irin wannan larura ta rashin lafiya.
Dokta Shu’aibu ya bayyana cewa, a da, idan mace kamu da ciwon yoyon fitsarin ta zo asibitin kwararru sai dai a tura ta Jos ko wani asibiti domin a yi mata magani domin ba”a yin jinyar a wurin su.
Ya ce a duk lokacin da matan ke fama da matsalar ba wai yoyon fitsari kadai ba, har ma da rashin bayan gida da ke hana su shiga cikin al’umma, Wanda hakan ke sa ana nuna musu wariya idan suka shiga taron jama’a.
A cewar sa, daga watan Satumba na shekarar 2024 zuwa yanzu, an yi wa mata 64 tiyatar Kuma kyauta.
Daga nan sai ya ce nan gaba kadan asibitin kwararru na jihar Gombe zai fara gudanar da aikin tiyatar yoyon fitsari kamar kowane irn jinya.
Wakilin hukumar UNFPA a wannan fanni, Dr Olanre Bajuwa, ya ce a kullum kokarin su na ganin yadda za su taimaka wa mata masu irin wadannan matsalolin.
Dakta Bajuwa ya ce bai ga dalilin da ya sa za”a na nuna wa matan wariya ba ko kuma a bar su su mutu saboda takaici saboda sun tsinci kansu a cikin irin wannan matsala.
Wasu daga cikin matan da suka ci gajiyar shirin jinyar sun yabawa hukumomi da gwamnatin jihar Gombe bisa tallafin da aka ba su.
Matan sun ce yanzu sun ji dadi kuma za su koma wurin mazajen su cikin koshin lafiya






