Ba Mu Goyon Bayan Kudurin Dokar Rage Karfin Sarkin Musulmi – Sakkwatawa

Sakkwatawan da suka halarci zaman sauraron ra’ayin jama’a akan kudurin dokar yiwa masarautar Mai alfarma Sarkin musulmi gyaran fuska da majalisar dokokin ta gabatar sun nuna adawa da kyamar wannan dokar.

Da yawa daga wakilan al’umma da suka halarci wannan zaman sun koka da rashin basu damar su bayyana ra’ayin su game da wannan dokar.

Sannan akasarin wadanda aka ba dama kamar tsohon dan majalisar wakilai kuma wakilin Kungiyar Sakkwatawa mu koma tushe Kakale Shuni, ya bayyana cewa idan dai har ba za a karawa Mai Alfarma Sarkin Musulumi karfin iko ba, to kuwa ba za a rage masa ba.

Shima da yake nasa bayani, wakilin Kungiyar Gidajen Sarauntar Sakkwato gaba dayan su Shehu Garba Takatuku, ya yi zargin cewa dukkanin wadanda aka ba damar suyi Magana ba ‘yan asalin jihar Sakkwato bane, dalibai ne da ke karatu a Sakkwato. Don haka yace ba zasu taba amincewa da wannan matakin ba.

Don haka yace ba za su taba amincewa da wannan kudurin ba, kuma zasu dauki akan dukkanin ‘yan siyasar dake wannan abun.

Shi kuma Magajin Garin Silame Alhaji Bandado Shehu Bande, duk da ance mutane su zo su bayyana ra’ayinsu, amma ba a basu dama ba, sun dai aikata abin da suke so, don haka ba da yawun Sakkwatawa za a gabatar da wannan dokar ba.

Tun da farko gwamnatin jihar ta ce zai yi gyara ne ga sashe na 76, kashi na biyu na dokar ƙananan hukumomin jihar ta shekarar 2008.

An riga an yi wa dokar karatu na farko da na biyu a wani zama da aka yi ranar Talatar makon jiya, inda ake sa ran da ƙudurin ya zama doka, ƙarfin ikon nadawa da cire hakimai da dagatai zai koma ƙarƙashin ikon gwamnan jihar Sokoto, maimakon Sarkin Musulmi.

Dokar ta shafi damar da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ke da ita, kan naɗa hakimai da dagatai kai tsaye, inda ikon hakan zai koma hannun gwamnan jihar da zarar dokar ta tabbata.

Sai dai lamarin na ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda jama’a da dama a Najeriya suka bayyana matakin da shirin rage ƙarfin ikon Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku.

Daga cikin waɗanda suka mayar da martini har da ƙungiyar Muslumi ta Najeriya Muric, da ta bayyana cewa taɓa kimar Sarkin Musulmin tamkar taba ruhin Musulman Najeriya ne

Related Posts

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo