Gwamnan Zamfara Ya Gayyato Masu Zuba Jari A Jihar

A Ziyarar da ya kai ƙasar ta Turkiyya a farkon watannan na Yuli, Gwamna Lawal ya samu ganawa da wasu masu zuba jari a ƙasar, tare da kai ziyarorin gani da ido a garuruwa daban-daban.

Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu yau a Gusau cewa, Gwamna Lawal ya fara wannan ziyarar aiki a ƙasar Turkiyya ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Yunin nan da ya gabata, inda ya kwashe kwana shida a can.

Sanarwar ta Malam Idris ta kuma bayyana cewa, gwamnan da muƙarraban sa, sun ziyarci wurare da dama, waɗanda suka haɗa da wuraren Kayan amfanin gona na zamani, wurin samar da nonon shanu, kiwon kaji da kamfanin ƙera motocin noma (Tarakta) na ‘Turk Traktor (tractors) manufacturing plant.’

“A wannan ziyarar aiki ta Turkiyya, Gwamna Lawal ya fara ne da kai ziyara a Bursa City, inda kamfanin Direkci Group ke da wurin Kayan amfanin gona na zamani mafi girma a ƙasar, inda shugaban kamfanin na Direkci Group, Mehmet Nurullah Direkçi, da kan shi ya zagaya da gwamnan cikin wannan katafaren wuri.

“Shi wannan kamfani na Direkci Group, ya na samar da harkokin noma ga ƙasar ta Turkiyya da sauran masu zuba jari ta hanyar kanyan amfanin gona na zamani. Kamfanin zai samar da irin wannan shirin kayan amfanin gona na zamani a jihar Zamfara.

“Idan wannan kamfani na Direkci Group ya shigo Zamfara, zai samar da kayan amfanin gona na zamani kala-kala, waɗanda suka haɗa da noman zamani mara iri, noman zamani mai iri, dashen shuka, noman ayaba na zamani dai sauran harkokin noma na zamani”

Yayin da yake a birnin Gaziantep, Gwamna Lawal ya ziyarci gonar noman madara ta Innova Dairy, wacce ke ba da shawarwari da sabbin hanyoyin kafawa da sarrafa gonakin zamani yadda ya kamata.

“Gonar ta Innova Dairy Farm za ta kafa wani tsari a Jihar Zamfara don amfani da duk fasahohin zamani da suka haɗa da Kiwon Shanu na Zamani, Tsarin Kula da Garken Dabbabi, Tatsar Madarar Shanu, Sarrafa Taki da kayan aikin gona.”

A Lardin Sakarya, Gwamna Lawal da tawagarsa sun ziyarci masana’antar sarrafa taraktoci ta TurkTraktor domin tantance tsarin samar da taraktocin da suka dace da noma a Nijeriya.

“A masana’antar Turk Traktor, Gwamna Lawal ya tattauna yiwuwar haɗin gwiwa da kamfanin domin ba iwa Jihar Zamfara damar samun waɗannan taraktoci na zamani.

“Turk Traktor yana da ikon samar da taraktoci ta zamani. Kamfanin dai shi ne kamfani na farko da ke fitar da taraktoci a ƙasar Turkiyya kuma ya kai kashi 88 bisa 100 na adadin taraktocin da ƙasar ke fitarwa a shekarar 2022.

“TurkTraktor babban kamfani ne na duniya, wanda ke fitar da taraktoci zuwa ƙasashe 125, kuma yana samar da kusan kashi 80 bisa 100 na adadin kayayyaki zuwa kasuwannin Arewacin Amurka da Turai.”

Related Posts

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum