Gwamnan Zamfara Ya Kashe Naira Biliyan 7 Ga Fansho Da Garatuti

Gwamna Dauda Lawal ya samu nasarar biyan haƙƙin ma’aikatan jihar Zamfara da na Ƙananan Hukumomi, waɗanda suka bar aiki, wanda ya zarta Naira Biliyan bakwai.

A watan Janairun wannan shekarar ne gwamnatin jihar Zamfara ta kafa wani kwamitin da zai tantance tsaffin ma’aikatan jihar da ba a biya su haƙƙin su na barin aiki ba, a tsakanin shekarar 2015 da 2024, da kuma bashin fanshon tsaffin ma’aikatan Ƙananan Hukumomi na tsakanin shekarar 2012 da 2019.

A cikin sanarwar da ya fitar yau a Gusau, Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an samu nasarar biyan bashin kuɗi N7,345,674,918.42 a biya bakwai da aka yi.

Sanarwar ta Sulaiman Bala ta ƙara haske da cewa wannan aiki na biyan basussukan tsaffin ma’aikatan, yana tafiya ba tare da wata tangarɗa ba.

Ya ce, “Gwamnatin jihar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta jajirce don ganin ta kammala biyan bashin tsaffin ma’aikatan jihar da na Ƙananan Hukumomi, wanda ya zarta Naira Biliyan 13.

“Abin takaici ne yadda gwamnatocin da suka gabata su ka bar tsaffin ma’aikatan cikin mawiyacin hali na ƙin biyan su haƙƙokin su na barin aiki, wanda alhamdu lillahi, yanzu Gwamna Lawal yana sallamar su.

“Yanzu dai waɗanda aka tantance su 1,926 cikin mutum 3,880 an biya su haƙƙoƙin su a biya bakwai da aka yi, wato kashi 1, 2, 3, 4, 5, da na 6, an biya su abin da ya kai ma tsabar kuɗi har N3,345,642,807.22, daga cikin N8,095,948,906.63 da ake bi.

“Kwanan nan ne aka biya kashi na bakwai, waɗanda suka kai su 215, wanda ya kai ma N499,886,578.77.

“A ɗaya ɓangaren kuma, an biya tsaffin ma’aikatan Ƙananan Hukumomi da Malaman makarantun Firamare su 3,513 a kashi bakwai, wanda ya kai ma N3,500,145,532.43.

“Za a ci gaba da wannan ƙoƙari, domin yana daga cikin shirin gwamnati na inganta harkar aikin gwamnati a jihar, don samar da ingantaccen aikin gwamnati.”

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum